Da Gaske Majalisa na Amincewa da Bukatar Tinubu Ta Karbo Bashi Ido Rufe? Bayanai Sun Fito
- Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce majalisa ba ta amincewa da duk buƙatar karɓar bashi kai tsaye
- Ya ce ‘yan majalisa na tantance buƙatun rance bisa tsarin kuɗaɗen gwamnati da suka amince da shi a baya
- Sanata Bamidele ya bayyana cewa duk buƙatun lamunin da gwamnatin Tinubu ta gabatar sun dace da tsarin da majalisa ta amince da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce Majalisar Tarayya ba ta amincewa da buƙatun karɓar bashi da bangaren zartarwa ke gabatarwa kai tsaye.
Sanata Bamidele ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa na tantance duk waya bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ciyo bashi bisa tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati da suka amince da shi a baya.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa Bamidele, wanda ke wakiltar mazabar Ekiti ta Tsakiya, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyi kan karuwar bashin da ake bin Najeriya.
Majalisa ta yi bayani kan karbo bashi
Shugaban masu rinjayen ya amince cewa majalisa ta amince da duk buƙatun karɓar bashi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar, amma ya ce hakan ba yana nufin ‘yan majalisa suna amincewa da duk buƙatar da bangaren zartarwa ya kawo ido rufe ba.
“Mun san damuwar ’yan Najeriya game da karbo aron kudi. Shin muna amincewa da duk buƙatun da bangaren zartarwa ke gabatarwa na karɓar bashi? Amsata ita ce a’a.
“Shin mun amince da duk buƙatun wannan gwamnati na karɓar bashi? Amsata ita ce eh,” in ji shi.
Ya bayyana cewa tsarin tantance buƙatun lamuni yana farawa ne da gabatar da tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati na matsakaicin lokaci (MTEF), takardar dabarun kasafin kuɗi (FSP) da kuma shirin karɓar bashi ga majalisa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Abin da doka ta tanada
Bamidele ya ce kundin tsarin mulki da dokar kula da kuɗaɗen gwamnati sun wajabta wa shugaban ƙasa gabatar da MTEF da FSP ga majalisa aƙalla kwanaki 30 kafin miƙa kasafin kuɗin sabuwar shekarar kuɗi.
Ya bayyana cewa takardun na fayyace hasashen kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma kaso na kuɗaɗen da za a kashe da ake sa ran za a samar ta hanyar kuɗaɗen shiga na cikin gida, rancen cikin gida da kuma lamunin ƙasashen waje.

Source: Facebook
Shugaban masu rinjayen ya ce ana yin waɗannan hasashe ne bisa wasu zato da ƙididdigar tattalin arziki, waɗanda za su iya sauyawa sakamakon abubuwan da ba a yi tsammani ba.
“Babban aikinmu shi ne mu koma ga tsarin kashe kuɗaɗen matsakaicin lokaci da takardar dabarun kasafin kuɗi da muka amince da su, domin tantance ko wannan rancen da suke son karɓa ya shiga cikin iyakokin abin da muka amince da shi.
“Idan ya dace da tsarin, za mu amince da shi. Idan bai dace ba, a lokacin ne za ku ji hayaniya. Tun da hakan bai faru ba, babu dalilin da zai sa mu ƙi amincewa, saboda mun riga mun amince da MTEF da FSP," in ji shi.
Bashin Najeriya ya kusa N200trn
Kun ji cewa a baya-bayan nan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirin karɓar bashi daga kasar waje, wanda ya kai kusan Naira tiriliyan 30.
Rahotanni sun nuna cewa idan shugaban kasar ya samu yadda yake so, jimillar bashin Najeriya na iya haura Naira tiriliyan 200 kafin ƙarshen 2026.
Asali: Legit.ng

