Tinubu Ya Tsawaita Hutun da Yake Yi a Kasar Waje, Ya Canza Ranar Dawowa Najeriya

Tinubu Ya Tsawaita Hutun da Yake Yi a Kasar Waje, Ya Canza Ranar Dawowa Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya a ƙarshen mako bayan ya ƙara tsawaita hutunsa na aiki da wasu ‘yan kwanaki
  • Tinubu ya tashi daga Najeriya zuwa London ranar 30 ga Agusta domin fara hutun aiki na makonni uku kamar yadda aka sanar
  • Yayin hutun, shugaban ya ci gaba da gudanar da harkokin ƙasa tare da ba da umarni kan wasu muhimman al’amura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya a ƙarshen mako, bayan ya ƙara tsawaita hutunsa na aiki da wasu ‘yan kwanaki.

Idan baku manta ba, Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta zuwa London domin fara hutun aiki, inda daga bisani ya wuce kasar Faransa.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da shugaban Faransa, Emmanuel Macron yayin wata liyafa a birnin Faris Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da tsawaita hutun da Tinubu ke yi a kasar waje a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC

Yadda Tinubu ke hutun aiki a waje

Bayan ya shafe mako guda a London, Tinubu ya wuce Paris, Faransa, inda ya gana da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da ɗan kasuwa, Mista Vincent Bollore.

Tun bayan fara hutun, Shugaba Tinubu ya ci gaba da tuntuɓar jami’an gwamnati da ke gida tare da bayar da umarni kan harkokin ƙasa.

Sanarwar ta ce daga cikin ayyukan da Tinubu ya bada umarni har da kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin binciken mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne a Minna.

Kashim Shettima ya wakilci Tinubu

A lokacin da yake hutun, Shugaba Tinubu ya ba Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima damar wakiltarsa a wasu tarukan gwamnati

Sai dai Shettima ya bar Abuja ranar 20 ga Satumba zuwa New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda shi ma ya kasance yana wakiltar shugaban a wasu taruka, zai ci gaba da yin hakan.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta barke kan Atiku ya kira Tinubu da sunan da 'bai dace ba'

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana zargin da Atiku Abubakar da wani kamfanin Amurka, suka yi kan rashin halartar taron Majalisar dinkin duniya da Shugaba Tinubu ya yi a matsayin zargi marar tushe kuma abin da ba shi da alhaki.

Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yayin da yake jagorantar taron Majalisar tattalin arziki (NEC) a Aso Rock Hoto: @OfficialSKSM
Source: Twitter

Shettima zai yi jawabi a taron UNGA

Ta ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ke wakiltar shugaban a babban taron na duniya, zai gabatar da jawabin Najeriya na ƙasa.

A cewar sanarwar:

"Mataimakin shugaban ƙasa Shettima, wanda ke wakiltar shugaban ƙasa a taron majalisar dinkin duniya, zai gabatar da jawabi a madadin Najeriya."

Dalilin tura Shettima taron UNGA

Kun ji cewa Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron UNGA a kasar Amurka.

Ya ce Shettima yana ɗauke da cikakken ikon Shugaban Ƙasa da na Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, yana mai watsi da ra’ayoyin cewa rashin Tinubu a taron zai rage martabar Najeriya a fagen diflomasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262