Kwankwaso Ya Ce Abba Kabir na Yunkurin Sa EFCC Ta Bincike Shi
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da kokarin jawo shi da iyalansa cikin ce-ce-ku-ce ta hanyar amfani da hukumomi
- Kwankwaso ya yi ikirarin cewa gwamnan ya taba kai korafi ga EFCC domin ta bincike shi, amma bayan hukumar ba ta bi bukatarsa ba, sai aka yi amfani da wata kungiya
- Ya kuma zargi gwamnan da wasu jami'an gwamnatinsa da amfani da kafafen yada labarai wajen bata masa suna da raunana damar 'yan takararsu a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da kokarin bata masa suna ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati, musamman Hukumar EFCC.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya nuna damuwarsa kan yadda alakar siyasa da ta kashin kai tsakaninsa da gwamnan ta koma cikin takaddama.

Kara karanta wannan
Siyasar Kano: NDC ta tsoma baki kan zarge zargen da Gwamna Abba ya ɗorawa Kwankwaso

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce Abba ya taba rike mukamai daban-daban a karkashinsa, ciki har da mataimakinsa na musamman, babban sakataren ofishinsa da kwamishina.
Kwankwaso ya tuna alakarsa da Abba
Tsohon gwamnan ya ce Abba ya kasance dan takarar da jagorancin tafiyarsu ta siyasa ya amince da shi a zaben 2019 da na 2023, inda ya samu nasara a zaben 2023 tare da goyon bayan tafiyar.
Kwankwaso ya ce sun shafe shekaru 43 suna da alaka, kuma ya dora masa amana, amma yana zargin an yi amfani da wannan amana ta hanyar da ba ta dace ba.
Ya yi ikirarin cewa gwamnan na kokarin jawo shi da iyalansa cikin takaddamar jama'a domin bata masa sunan da ya kwashe kusan shekaru 50 yana ginawa.
Ya zargi Abba da neman amfani da EFCC
Kwankwaso ya yi ikirarin cewa watanni da suka gabata gwamnan ya gabatar da bukata a hukumance ga EFCC domin ta bincike shi.
A cewarsa, bayan hukumar ta kasa bin wannan bukata saboda ka'idojinta da mutuncin aikinta, sai aka koma amfani da wata kungiya mai suna SACGGI.
Ya yi ikirarin cewa kungiyar ba ta da rajista da CAC, kuma ba ta da wata sahihiyar kafar sadarwa ko alaka ta hukuma da EFCC ko Hukumar ICPC.
Kwankwaso ya ce an yi amfani da kungiyar wajen shirya zanga-zanga a harabar ofishin EFCC domin matsa wa hukumar lamba.
Maganar Kwankwaso kan 2027
Kwankwaso ya kuma zargi gwamnan da kokarin yin tasiri kan wasu hukumomi, ciki har da INEC da bangaren shari'a, domin hana Aminu Abdussalam, dan takararsu na gwamnan Kano, shiga zaben 2027.
Ya ce Abdussalam na kare tikitinsa a gaban INEC da kotuna, yana mai zargin cewa ana kokarin hana wallafa sunansa a matsayin dan takara domin gwamnan ya tsaya takara ba tare da abokin hamayya ba.
Tsohon gwamnan ya ce irin wadannan matakai na iya kara zafafa siyasa da kuma raunana zaman lafiya da tsaro a jihar Kano.
Ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a siyasa da su mutunta 'yancin hukumomin gwamnati, tare da gujewa duk wani abu da zai rage amincewar jama'a da su.

Source: Facebook
Kwankwaso ya kare kan shi
A cikin sanarwar, Kwankwaso ya gode wa EFCC kan yadda ta gudanar da gayyatar da ta taba yi masa sau biyu a lokacin da yake rike da mukaman gwamnati.
Ya ce bayan ya bar gwamnatin Kano sama da shekaru 11 da suka gabata, yana alfahari da cewa ya ci gaba da kasancewa da tarihin aiki mai kyau.
Ya lissafa mukaman da ya taba rike wa, ciki har da gwamnan Kano na tsawon shekaru takwas, aikin gwamnati na shekaru 17, mataimakin shugaban majalisar wakilai a Jamhuriya ta Uku, ministan tsaro da kuma sanata a majalisa ta takwas.
Ya kuma shawarci matasa da masu rike da mukaman gwamnati da su yi taka-tsantsan, yana mai cewa mukaman gwamnati ba na dindindin ba ne.
Bwala ya soki Obi da Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa ta siyasa, Daniel Bwala, ya yi watsi da yiwuwar Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2027.
Bwala ya bayyana Obi a matsayin shugaban kafafen sada zumunta, yana mai cewa farin jinin da yake da shi a intanet ba lallai ne ya koma kuri'u a akwatin zabe ba.
Ya kuma yi ikirarin cewa yanayin siyasar da ya taimaka wa Obi a zaben 2023 ya sauya, sannan ya ce Rabiu Kwankwaso ma ya san cewa ba za su yi nasara a zaben 2027 ba.
Asali: Legit.ng


