Farfesa Ya Kunyata Atiku da Kin Karbar Aiki a Kwamitin Yakin Zaben ADC

Farfesa Ya Kunyata Atiku da Kin Karbar Aiki a Kwamitin Yakin Zaben ADC

  • Kingsley Moghalu ya ce ba a nemi amincewarsa ba kafin a sa sunansa cikin kwamitin tsare-tsare a kamfen Atiku Abubakar
  • Tsohon mataimakin gwamnan na CBN ya daina siyasar jam'iyya tun a shekarar 2022 kuma bai goyon bayan wani bangare
  • Kwamitin yakin zaben na Atiku ya kunshi manyan 'yan siyasa, Moghalu ne wanda aka fara ji ya barranta kanta daga gare su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kingsley Moghalu ya ki karbar aikin da Atiku Abubakar ya ba shi na taya shi yi masa kamfen a zaben shugaban kasa.

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN ya bayyana cewa an sa shi cikin kwamitin kamfen ADC ba tare da an tuntube shi ba.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi da Kingsley Moghalu Hoto: @Atiku/@MoghaluKingsley
Source: Twitter

Kingsley Moghalu ya tanka Atiku Abubakar

A wani jawabi da ya fitar a shafin X Kingsley Moghalu ya ce ya yi mamakin ganin sunan shi a kwamitin.

Kara karanta wannan

Naja da sauran mata 10 da suka samu shiga kwamitin yakin neman zaben Atiku

Atiku Abubakar ya sa masanin tattalin arzikin a cikin kwamitin tsara manufofi na yakin neman zaben shugaban kasa a 2027.

Mohammed Hayatu-Deen wanda ya nemi tikiti tare da Atiku ADC shi ne shugaban kwamitin.

Farfesa Moghalu ya ce ba a yi magana da shi ba kuma bai bada amincewarsa ba kawai aka jefa shi a harkar tallar jam’iyyar ADC.

A wannan jawabi na ranar Alhamus, Moghalu ya ce bai cikin tafiyar a hukumance ko kuma a matsayin mai bada shawara daga gefe.

“Ba a tuntube ni ba, kuma ban bada umarnin a wallafa sunana a matsayin ‘dan kwamitin tsara manufofin ‘dan takaran ADC ba.
"Kai asali ma, ban cikin ‘yan kwamitin tsara manufofin Atiku ko da a matsayin mashawarci ne."

Moghalu ga Atiku: "Na daina siyasar jam'iyya'

Shi ma Moghalu ya taba tsayawa neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar YPP, amma Muhammadu Buhari ya doke su a 2019.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur

Moghalu ya ce tun 2022 ya yi sallama da siyasar jam’iyya a cewar rahoton jaridar The Cable.

“Ni ba ‘dan wata jam’iyyar siyasa ba ne kuma ban tare da kowa a Najeriya.”

- Kingsley Moghalu

Masanin tattalin ya ce aikin gaban sa shi ne shugaban cibiyar IGET da take kokarin kawo sauyin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Haka zalika shi ne shugaban cibiyar Sogato Strategies mai kawo shawarwarin tattali a duniya.

IGET da Sogato Strategies ba su da alaka da wata jam’iyyar siyasa, kamar yada Moghalu ya ce burinsa shi ne cigaban kasarsa.

“Ina ci gaba da kasancewa mai kishin kasata, Najeriya, da ci gabanta, amma irin wannan kishin ba ya nufin dole sai na kasance cikin kowace irin alakar siyasa da wata jam’iyya ba,”

Yake cewa shi ya zabi ya fi tafarkin zama dattijo, ba nuna bangarancin siyasa a Najeriya ba.

Matan da ke gaba wajen tallar Atiku a ADC

Labari ya gabata cewa Atiku Abubakar ya sa Naja’atu Mohammed cikin ‘yan kwamitin yakin zaben shugaban kasa da za a yi a 2027.

Kara karanta wannan

Matashin da aka sa a kwamitin yakin zaben Obi da Kwankwaso ya cire kan shi

Tsofaffin ‘yan Obidient irinsu Nana Kazaure da Rhoda Sanda za su tallata takarar ADC, suna cikin mata 10 da suka samu shiga cikin kwamitin.

Lauretta Onochie da Zainab Buba Galadima da suka yi aiki gwamnatin ADC sun canza gida, wannan karo suna tare da jam'iyyar hamayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng