2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

  • Kingsley Moghalu, tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar YPP ya koma ADC
  • Tsohon mataimakin gwamnan na CBN ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a a dandalin sada zumunta
  • Moghalu ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga magoya bayansa da suka shiga jam'iyyar ta ADC

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Kingsley Moghalu ya koma jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) gabanin babban zaben 2023.

Kingsley Moghalu ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook a ranar Juma'a inda ya rubuta cewa, "An kammala komai a hukumance."

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya
Kingsley Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma ADC. Hoto: Kingsley Moghalu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya kuma wallafa wata sabuwar fosta dauke da hotonsa da tambarin sabuwar jam'iyyarsa.

Ya ce:

"Na yi imanin za mu iya sauya tsarin tattalin arzikin Nigeria ta sanannun hanyoyi na zamani da fasahar matasan Nigeria. Ina kira ga dukkan magoya baya na su shiga jam'iyyar ADC."

Moghalu ya yi takarar shugabancin kasa a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar YPP inda ya samu kuri'u 26,039.

Shi ne ya zo na 14 a jerin yan takarar shugaban kasar.

Legit.ng za ta iya tunawa cewa a yayin da ya ke magana game da abin da zai aiwatar a Nigeria idan an zabe shi, Moghalu ya yi alkawarin cewa zai kafa gwamnatin da za ta magance rashin tsaro.

Ya cigaba da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an inganta ilimi da sauye-sauye a bangaren lafiya sannan zai yi yaki da talauci da hanyar inganta tattalin arziki.

Tsohon ma'aikacin na CBN ya yi takara a tare da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, Atiku Abubakar na PDP da wasu da suka yi takarar a 2019.

Kara karanta wannan

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

2023: Zan yi takarar shugaban kasa a 2023, Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Moghalu ya sanar

Hakan na zuwa ne kimanin watanni hudu bayan Moghalu ya sanar da niyyarsa na shiga takarar shugabancin kasa a 2023.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na YPP a 2019, ya sanar da hakan ne a ranar Talata 1 ga watan Yuni a dandalin sada zumunta.

Sanarwar da ya fitar an yi mata lakabi kamar haka, 2023: Zan yi takara saboda al'umma na da muhimmanci.

Ya ce:

"Babu alamar kawo karshen matsalolin mu har sai Nigeria ta duba batun samun shugabanci na gari ta fara neman cancanta, kwarewa da mai tausayin talaka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel