Kwankwaso Ya Gano Abin da Ya Sa Yan Najeriya ke Shan Wahala bayan Cire Tallafin Fetur

Kwankwaso Ya Gano Abin da Ya Sa Yan Najeriya ke Shan Wahala bayan Cire Tallafin Fetur

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso ya ce cire tallafin man fetur ya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin matsala
  • Tsohon gwamnan na Kano ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta cire tallafin ba tare da tanadin rage wa ’yan Najeriya radadin matakin ba
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ’yan Najeriya sun cancanci sayen man fetur cikin rahusa sabsnin farashin da ake sayar wa a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi maganar halin da yan Najeriya ke ciki na wahalhalu.

Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa yake ganin cire tallafin man fetur da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ya jefa tattalin arzikin Najeriya da al'ummar kasar cikin matsala.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya fadi gaskiya, ya ce farashin man fetur zai iya ƙara tsada a Najeriya

Kwankwaso RM.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya tabo wadannan bstutuwa ne yayin wata hira da ska yi da shi a tashar Arise TV jiya Talata, 23 ga watan Satumba, 2026.

Kwankwaso ya dora laifi kan Tinubu

Kwankwaso ya ce Tinubu ya cire tallafin bayan hawansa kan mulki ba tare da samar da matakan da za su rage wa ’yan Najeriya radadin da matakin zai iya haifarwa ba.

Ya ce an ɗauki matakin ba tare da la’akari da illolin da ka iya biyo bayansa ba, lamarin da a cewarsa ya ƙara haifar da matsalolin tattalin arzikin ƙasar da tsadar rayuws da jama'a ke ciki.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma abokin takarar Peter Obi a zaben 2027, ya ce an cire tallafin ba tare da ɗaukar matakan rage wa jama’a tasirin matakin ba.

Kwankwaso ya soki hanyar cire tallafi

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito Kwankwaso na cewa:

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, sama da 67% na yan Najeriya na so a dawo da tallafin fetur

“Shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar cire tallafin man fetur kuma illolin da muka yi tsammanin za su faru, tabbas sun faru.
“Ya cire tallafin nan take ba tare da duba dukkan matsalolin da ka iya tasowa ba. Hakan ne ya jefa mu cikin wannan babbar matsala ta tattalin arziki,” inji shi.

Kwankwaso ya kuma dage kan cewa ’yan Najeriya sun cancanci sayen man fetur a farashi mai rahusa.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wannan kalamai na Kwankwaso na zuwa ne yayin da ake tsaka da ce-ce-ku-ce kan batun dawo da tallafin mai a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar ADC, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin dawo da tallafin mai idan ya aka zabe shi ya zama shugaban Najeriya a zaben 2027.

Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafi

A wani labarin, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin NDC ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban da tsarin da aka sani a baya ba.

Da aka tambaye shi yadda za a aiwatar da hakan, Kwankwaso ya ce gwamnati za ta iya zuba jari wajen matatun mai domin ƙara samar da fetur a cikin gida, ta yadda za a samu man fetur ga ’yan Najeriya a farashi mai sauƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262