Me Ya Yi Zafi? Gwamna Ya Tsige Kwamishina, Ya Kore Shi daga Aiki Nan Take
- Gwamna Francis Nwifuru ya tsige Kwamishinan Ayyuka na jihar Ebonyi, Engr. Stanley Lebechi Mbam, daga mukaminsa nan take
- Gwamnan ya umarce shi da ya mika kadarorin gwamnati da ke hannunsa, ciki har da motar aikinsa sannan ya bar ofis ba tare da bata lokaci ba
- Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar gwamnatin kan jinkirin da aka samu wajen kammala wasu ayyukan gine-gine da take gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi, Nigeria - Gwamnan jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Francis Nwifuru, ya tsige Kwamishinan Ayyuka na jihar, Engr. Stanley Lebechi Mbam, daga mukaminsa nan take.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar ma’aikatan gwamnati da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Dr Monday Uzor, ya sanya wa hannu ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan
Mabiyan Sheikh Lukuwa sun kawo cikas a matakin da aka ɗauka kan taɓa iyayen Annabi SAW

Source: Twitter
Gwamna Nwifuru ya kori kwamishina daga aiki
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a sanarwar, Gwamna Nwifuru ya umarci Injiniya Mbam da ya mika dukkan kadarorin da kayan aikin mallakin gwamnati da ke hannunsa.
Gwamnan ya umarci tsigaggen kwamishinan da ya mika motar da aka ba shi domin gudanar da aikinsa, ga Sakataren Gwamnatin Jihar Ebonyi, kana ya tattara kayansa ya bar ofis.
Mai girma gwamna Francis Nwifuru ya kuma umarce shi da ya mika takardu da sauran nauye-nauyen aiki da ke kansa ga Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka.
Ko me ya sa gwamnan ya dauki mataki?
Sanarwar ta ce:
“Gwamnan jihar Ebonyi, Mai Girma Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru, FNIOB, FCAI, GGCEHF, ya bayar da umarnin tsige Kwamishinan Ayyuka, Engr. Stanley Lebechi Mbam, daga mukaminsa nan take.”
Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa da gwamnan ko wanai daga cikin jami'an gwamnatinsa da ta bayyana wani dalili na tsige kwamishinan, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Sokoto: Sunayen malamai da za su tantance kalaman Sheikh Musa Lukuwa kan Annabi SAW
Ana zargin jinkirin ayyukan gwamnati
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar gwamnatin jihar Ebonyi kan jinkirin da aka samu wajen kammala wasu ayyukan gine-gine da take gudanarwa a sassan jihar.
Sai dai gwamnan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da ingantaccen shugabanci da bunkasa ababen more rayuwa ga jama’a.

Source: Facebook
Bayan tsige Mista Mbam, ana sa ran Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka ta jihar Ebonyi zai kula da harkokin ma’aikatar har sai gwamnatin jihar ta ba da wasu umarni.
Gwamnan Ebonyi ya ja kunnen ciyamomi
A wani labarin na daban, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya umarci sababbin shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar jam'iyyar APC ta lashe yankunansu a zabe mai zuwa.
Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa umarnin nasa ba barazana ba ce ga jam’iyyun adawa, sai dai nuna jajircewarsa wajen kare APC da tabbatar da nasararta a jiharsa.
Gwamnan ya kuma bukaci shugabannin su sasanta da abokan hamayyarsu, yayin da ya nemi a ba mata da matasa damar samun naɗin mukaman gwamnati
Asali: Legit.ng