Tsadar Mai: Rarara Ya Yi Katobara kan Tinubu, Ya Ce ana Kukan Dadi a Najeriya

Tsadar Mai: Rarara Ya Yi Katobara kan Tinubu, Ya Ce ana Kukan Dadi a Najeriya

  • Mawakin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya kara ba gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu kariya yayin da aka fara magana kan zaben 2027
  • A bayanin da ya yi, Rarara ya bayyana cewa ba shi da ilimi a harkar man fetur da tattalin arziki, amma ya san kukan dadi ake a Najeriya
  • Hakan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke korafi kan tashin farashin man fetur, inda dan takarar ADC, Atiku Abubakar ya ce zai maido tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya sanar da cewa ya kaddamar da yi wa Bola Tinubu da APC kamfen a zaben 2027.

Mawakin ya yi magana kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya, inda ya ce ana ruruta matsalolin da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Matsayar addinin Musulunci kan sayen hannun jarin matatar Dangote

Rarara da Bola Ahmed Tinubu
Dauda Rarara a hagu, Bola Ahmed Tinubu a dama. Hoto: Dauda Kahutu Rarara|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi kuma tashar ta wallafa bidiyon a shafinta na Facebook.

Rarara ya ce ana kukan dadi

A game da tsadar man fetur, inda lita ta haura N1,500, Rarara ya bayyana cewa yana goyon bayan Tinubu ne saboda ya kuduri gyara kasa.

Ya ce:

'Shi Tinubu ba ya karya, ba ya yaudara,'

Ya kara da cewa shi ba shi da masaniya a kan harkar NNPCL ko harkar mai, ya ce a yanzu yaki ake a Iran amma dai ya ce duk da haka akwai saukin mai a Najeriya.

Ya ce:

'Mu nan kasan yawanci kukan dadi muke yi, kasan da kukan yunwa ake ki."

Rarara ya kara da cewa Bola Tinubu bai yaudari kowa ba kuma ya san gyara ake saboda haka ana cigaba da gyara, inda ya ce yanzu taki ake fata ya sauko kuma shi ma zai yi kasa.

Kara karanta wannan

Yadda Dangote ya yi shekara 36 yana zaune a gida 1 ba tare da sauya shi ba

Dauda Kahutu Rarara
Rarara na amsa wayar tarho. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Batun bude kamfen

Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa ya kaddamar da kamfen domin goyon bayan APC, inda ya ce hakan yana da muhimmanci.

A amsar da ya bayar game da dalilin kaddamar da gangamin, Rarara ya bayyana cewa ba kowane dan siyasa ba ne zai iya kaddamar da kamfen a yi taro a gama lafiya a halin da ake ciki.

Maganar tallata Tinubu a Najeriya

Dauda Rarara ya bayyana cewa yanzu mutane da yawa na tallaa Bola Tinubu alhali da shi kadai ya ke yi a Najeriya.

Mawakin ya kara da cewa Bola Tinubu yana duba abubuwan da suke faruwa a yau ne domin kafa tubalin da zai amfani kasa nan da shekaru da yawa masu zuwa.

Ya bayyana cewa yana tallata APC ne ba wai saboda kudi ba, ya ce shi ba mawakin neman kudi ba ne, ya ce ba wani kudi aka ba shi ya yi tallan marigayi Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

'Ban taɓa fitar da Zakkah ba': Sarkin Zazzau ya faɗi abin da ya fi ba muhimmanci

APC ta caccaki Wike

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta nuna rashin gamsuwa da bayanan da ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi.

Shugaban APC na jihar Bayelsa ya bayyana cewa ba su bukatar hada kai da kawancen Wike domin samun nasara a yankunan jihar.

Martanin APC ya biyo bayan wasu maganganu da Wike ya yi ne game da siyasar 2027, inda ya bayyana cewa yana da tsari mai karfi a Rivers da Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng