Zance Ya Kare: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci kan Soke Rajistar Jam'iyyar NDC
- Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yanke hukunci kan soke rajistar jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya
- Tun da farko NDC ta shigar da kara kotun ne bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya da ya soke rajistar ta
- Jam’iyyar ta taya mambobinta da ’yan takararta murna, tare da kira gare su da su mayar da hankali kan yakin neman zabe da shirye-shiryen zabubbuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, wanda ya shafi rajistar jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce hukuncin Kotun Tarayya da Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke watanni kadan da suka gabata, an soke shi.

Source: Facebook
Jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Juma'a, 18 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Tirkashi: APC ta yi zarge zarge masu nauyi kan Atiku, ta bukaci ya janye daga takara
Kotun ta amince da karar NDC
A cewar sanarwar, Mai Shari’a Mohammed Danjuma ne ya jagoranci zaman kotun, yayin da Mai Shari’a Hassan ya karanta hukuncin.
Kotun ta amince da karar da NDC ta shigar tana kalubalantar hukuncin Kotun Tarayya da ke Lokoja, sannan ta soke hukuncin da Mai Shari’a Dashen ya yanke.
NDC ta yi amfani da damar wajen yabawa bangaren shari’a na Najeriya, musamman Mai Shari’a Danjuma da Mai Shari’a Hassan, bisa abin da ta bayyana a matsayin kare martabar bangaren shari’a.
Jam’iyyar ta ce hukuncin ya kara bude damar shiga siyasa karkashin tsarin jam’iyyu da dama a Najeriya.
NDC ta ce rajistarta tana nan daram
NDC ta ce tun farko an kafa jam’iyyar ne domin fadada tsarin dimokuradiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya.
Ta bayyana hukuncin Kotun Tarayya da ke Lokoja da cewa ya zama abin mamaki kuma ya shafi ’yancin da kundin tsarin mulki ya bai wa jam’iyyar na shiga harkokin siyasa.

Kara karanta wannan
Gwamna a Najeriya ya kamu da rashin lafiya har ya gaza fitowa aiki? Gaskiya ta bayyana
Sai dai jam’iyyar ta ce hukuncin Kotun Daukaka Kara ya kare damar siyasa, tare da tabbatar da ’yancin NDC na shiga dukkan harkokin siyasa a matsayin jam’iyyar da aka yi wa rajista.
Jam’iyyar ta ce za ta shiga zabubbukan 2027
NDC ta taya dukkan mambobinta da ’yan takararta murna, tare da gode wa ’yan Najeriya bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba jam’iyyar.
Ta ce bayan hukuncin Kotun Tarayya na farko, ta samu kiraye-kirayen neman goyon baya da addu’o’i daga mutane daban-daban.
NDC ta jaddada cewa rajistarta tana nan cikin inganci, kuma ita da dukkan ’yan takararta za su shiga dukkan zabubbukan da za a gudanar a 2027 da kuma bayan haka, da yardar Allah.
NDC ta mayar da hankali kan yakin neman zabe
Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da su mayar da hankali kan yakin neman zabe, shirye-shiryen zabuka da sauran ayyukan da ke gabansu.
NDC ta ce ta dogara ne da sakonta, jajircewar mambobinta, ’yan takararta da kuma goyon bayan da ta ce take samu daga ’yan Najeriya.
Jam’iyyar ta bayyana cewa tana da kyakkyawan fata kan zabubbukan da ke tafe, tare da cewa za ta yi kokarin samun nasara a rumfunan zabe.

Kara karanta wannan
Dickson: Jagoran NDC na kasa ya fadi dalilin kin shiga APC, ya aika sako ga Kwankwaso da Obi

Source: Facebook
An farmaki magoya bayan NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu magoya bayan Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun fuskanci hari a jihar Delta.
Ana dai zargin wasu 'yan daban siyasa ne suka farmaki magoya bayan na jam'iyyar NDC, lokacin da suke gudanar da wani gangami a birnin Warri.
Asali: Legit.ng