An Sake Rusa Lissafin Tinubu, Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki Ya Fice daga Jam'iyyar APC
- Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Adamawa, Rt. Hon. Kabiru Mijinyawa, ya fice daga APC tare da dubban magoya bayansa
- Mijinyawa, wanda ke wakiltar mazaɓar Yola ta Kudu, ya koma jam’iyyar adawa ta APM yayin da ake shirin zaben 2027
- Ya ce rashin bin doka da rashin gaskiya wajen mu’amala da mambobin APC ne suka sa ya bar jam’iyya mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Nigeria - Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa kuma ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Yola ta Kudu, Alhaji Kabiru Mijinyawa, ya fice daga jam’iyyar APC.
Shugaban majalisar dokokin ya tabbatar da barin APC tare da dubban magoya bayansa zuwa APM ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, 2026.

Source: Facebook
Punch t ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban APC na jihar Adamawa, mai ɗauke da kwanan wata 13 ga Satumba, 2026.
Tsohon kakakin Majaliss ya bar APC
A wasikar, tsohon kakakin ya ce rashin bin doka da rashin gaskiya wajen mu’amala da mambobin jam’iyyar ne suka tilasta masa barin APC.
“Zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar kwanan nan a jihar Adamawa ya nuna cewa jam’iyyar ba ta da dimokuraɗiyyar cikin gida; an zaɓi wasu mutane a matsayin ‘yan takara ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba,” in ji shi.
Ficewar tsohon kakakin daga APC ta zo ne kwanaki biyu bayan ɗaruruwan jiga-jigan jam’iyya mai nulki ƙarƙashin jagorancin Alhaji Tahir Shehu, sun koma APM, cewar rahoton Daily Trust.
Shawarar da aka ba APC tun farko
Shehu, wanda ya yi magana a taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a gidan gwamnati ranar Asabar da ta gabata, ya shawarci shugabannin jam’iyyar da su gaggauta sasanta mambobin da suka fusata.
Ya ce:
“Domin mu shiga babban zaɓe a matsayin iyali ɗaya da ke da haɗin kai, akwai buƙatar gaggawa ta sasanta mambobin jam’iyyar da suka fusata.

Kara karanta wannan
Magana ta kare, INEC ta fitar da sunayen yan takarar shugaban ƙasa na ƙarshe kafin zaben 2027
"Ba sa neman wani abu, sai dai shugabannin jam’iyyar su nuna musu cewa suna daga cikin muhimman ɓangarorin APC a jihar Adamawa.”
Abin da ya jawo rikicin APC a Adamawa
Ficewar jiga-jigan APC ta ƙara ɗaga zafin siyasa a jihar, musamman bayan Alhaji Abdulraman Haske ya karɓi tikitin takarar gwamna na APM.
An yi zargin cewa Haske ne ya lashe tikitin takarar gwamna na APC, amma daga baya aka maye gurbinsa da Alhaji Ahmad Galadima.
A mazabar Sanatan Adamawa ta Tsakiya, an maye gurbin Abdulraman Abbati, wanda ke neman kujerar ba tare da hamayya ba, da Alhaji Salihu Mustapha, ɗan takarar neman gwamna.

Source: Twitter
A mazabar Sanatan Adamawa ta Kudu kuma, an maye gurbin Peter Fwa, wanda shi ma yake neman kujerar ba tare da hamayya ba, da Felix Tangwami, ɗan takarar neman gwamna.
Gwamnan Adamawa ya kare Tinubu
Kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi kira ga shugabannin shiyyar Arewa da su daina ɗaura wa Bola Tinubu laifi kan matsalar tsaro.
Fintiri ya ƙalubalanci shugabannin Arewacin ƙasar da su fuskanci gaskiya tare da neman mafita mai dorewa maimakon tsayawa suna zargin gwamnatin tarayya
Asali: Legit.ng
