Gwamna a Najeriya Ya Kamu da Rashin Lafiya har Ya Gaza Fitowa Aiki? Gaskiya Ta Bayyana
- Jam’iyyar APC reshen Jihar Ekiti ta karyata wani rahoto kan lafiyar Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji, tana mai neman a janye rahoton nan take
- Jam’iyyar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da hasashe da ba shi da tushe, tana mai cewa an yi shi ne domin tayar da hankalin jama’a
- APC ta ce Oyebanji yana cikin ƙoshin lafiya kuma zai fara wa’adinsa na biyu a ranar 16 ga Oktoba 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ado-Ekiti — Jam’iyyar APC reshen Jihar Ekiti ta karyata wani rahoto da ya shafi lafiya da matsayin Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji, tana mai neman a janye rahoton nan take.
APC ta maida martanai kan labarin cewa gwamnan na kwance ba shi da lafiya a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Segun Dipe, ya fitar ranar Alhamis.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce APC ta bayyana rahoton a matsayin “hasashe, ƙarya tsantsa da kuma zato marar amfani” da ake zargin an yi shi domin yaudarar jama’a da kuma tayar da hankalin mazauna jihar.
Jam’iyyar ta ce rahoton ba shi da wata hujja, kuma ya saɓa wa ƙa’idojin aikin jarida na gaskiya, tana zargin waɗanda suka wallafa shi da ƙoƙarin jefa jama’a cikin fargaba kan lafiyar gwamnan.
Sai dai APC ba ta bayyana sunan rahoton ko wanda ya wallafa shi ba a cikin sanarwar.
Wane hali Gwamna Oyebanji ke ciki?
Jam’iyyar ta ce:
“Domin kauce wa shakku, Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji yana cikin ƙoshin lafiya, yana cikin walwala, kuma ya mayar da hankali sosai wajen samar da shugabanci nagari ga al’ummar Jihar Ekiti.”
APC ta dage cewa babu ko ɗigon gaskiya a cikin rahoton, kana ta buƙaci mazauna jihar da ’yan asalin Ekiti da ke zaune a ƙasashen waje su kwantar da hankalinsu tare da yin watsi da abin da ta bayyana a matsayin labaran ƙarya.

Kara karanta wannan
Kwankwaso da Obi sun zo da wani tsari da zai iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027
APC ta sake goyon bayan gwamna
Jam’iyyar ta sake jaddada goyon bayanta ga Oyebanji, tana mai cewa gwamnan ya ci gaba da mayar da hankali wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnatinsa.
APC ta kuma ce za a rantsar da gwamnan domin fara wa’adinsa na biyu a ranar 16 ga Oktoba 2026, bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 20 ga Yunin da ya gabata.

Source: Getty Images
Jam’iyyar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Oyebanji tare da yin watsi da abin da ta bayyana a matsayin ƙoƙarin haifar da fargaba marar dalili a jihar Ekiti.
Gwamnan Ekiti ya ziyarci Tinubu
Kun ji cewa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya kai wa Bola Ahmed Tinubu ziyarar farko a fadar shugaban kasa tun bayan lashe zaben gwamnan da aka yi.
Biodun Oyebanji ya dauki alwashin ganin shugaban kasar da APC sun samu kuri’u 600, 000 zuwa 700, 000 a zaben shekarar 2027
Asali: Legit.ng
