Musulunci Ya Yi Rashi a Najeriya, Babban Limami Kuma Dan Kasuwa Ya Kwanta Dama
- Alhaji Abdul Mutalib Badamosi, limamin Masallacin Yatbawa da ke Ibagwa-Aka, Jihar Enugu, ya rasu kuma an binne shi bisa tsarin addinin Musulunci
- Marigayin shi ne babban shugaba (CEO) na kamfanin SMO Motors kuma fitaccen ɗan kasuwa da jagoran al’umma a Igbo-Eze South
- Shugaban Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze South, Ugo Ferdinand Ukwueze, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Jihar Enugu – Alhaji Abdul Mutalib Badamosi, limamin Masallacin Juma'a na Yarbawa da ke Ibagwa-Aka, Jihar Enugu, ya rasu.
Legit.ng ta tattaro cewa an binne Badamosi bisa tsarin jana’izar Musulunci. Marigayin ya kuma kasance babban dan kasuwa kuma shugaban kamfanin motoci na SMO Motors.

Source: Facebook
Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Ali Chikwudi ya tabbatar da wannan rasuwa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Zargin cin kudi ya kai ‘dan takaran APC a zaben majalisa cikin ragar hukumar ICPC
Baya ga rawar da yake takawa a fannin addini, an san Badamosi a matsayin jajirtaccen jagoran al’umma kuma ɗan kasuwa a Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze South.
Marigayin malamin addinin kuma ɗan kasuwar kawun Alhaji Jimoh Rauf Badamosi ne, wanda shi ne shugaban JRB Group kuma aka bayyana shi a matsayin fitaccen mai taimakon jama’a.
Ukwueze ya yi jimamin Badamosi
Shugaban Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze South, Ugo Ferdinand Ukwueze kuma mataimakin shugaban ALGON na Jihar Enugu, ya ziyarci iyalan Badamosi tare da isar da saƙon ta’aziyya, inda ya bayyana rasuwar a matsayin “babban rashi”.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 15 ga Satumba, Ukwueze ya ce:
“Na karɓi labarin rasuwar Alhaji Abdul Mutalib Badamosi cikin matuƙar baƙin ciki. Shi ne limamin Masallacin Yarbawa da ke Ibagwa-Aka, kuma jagoran addini da al’umma da ake girmamawa.
"Ya kasance fitaccen ɗan kasuwa kuma shugaban kamfanin SMO Motors, wanda rayuwarsa ta kasance cike da hidima da sadaukarwa ga jin daɗin al’ummarsa.”
Limamin yana matsayi mai girma
Ya ƙara da cewa Badamosi yana da “matsayi mai girma na girmamawa da ƙauna a tsakanin al’ummar Igbo-Eze South."
Ukwueze ya ce ziyarar da ya kai wa iyalan ta sa ya ƙara fahimtar girman rashin, inda ya ce:
“A irin wannan lokaci, kalmomi kan kasa isar da sako yadda ya kamata wajen bayyana girman wannan rashi, musamman idan mutum da ya sadaukar da wani muhimmin ɓangare na rayuwarsa wajen bautar Allah, kula da iyalinsa da yi wa al’ummarsa hidima ya rasu kwatsam.”

Source: Original
Ya isar da ta’aziyyarsa a madadin Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze South, inda ya ce:
“A madadin Gwamnati da al’ummar Igbo-Eze South baki ɗaya, ina miƙa saƙon ta’aziyyarmu mafi zurfi ga iyalan Badamosi da daukacin al’ummar Musulmi.
“A wannan lokaci na jimami, Allah Maɗaukaki Ya ba iyalan ƙarfin hali da juriyar jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.”
Uwa ga Sarkin Musulmi ta kwanta dama
Kun ji cewa gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya jajanta wa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III kan rasuwar kishiyar mahaifiyarsa, Hajiya Nana Asma’u.
Rahotanni sun nuna cewa Nana Asma’u ta rasu ne ranar Talata da ta gabata tana da shekara 100 a duniya.
Asali: Legit.ng

