Maganar Dawo da Tallafi na Taɓa Tinubu, Ya Tona wa Atiku 'asiri' kan Matatun Mai
- Fadar Shugaban Ƙasa ta soki shawarar Atiku Abubakar kan tallafin samar da fetur, tana cewa irin tsarin ya gaza a mulkinsu
- Mataimakin shugaban ƙasa na wancan lokaci Atiku ya fuskanci suka bayan bayanan da ke nuna cewa tallafin bai inganta amfani da matatun mai ba
- O’tega Ogra ya ce tallafin ya gaza hana tashin farashin fetur, tare da zargin cewa shirin ya samar da attajirai a tsakanin wasu mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da shawarar ɗan takarar ADC na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan samar da tallafin ga matatun mai na cikin gida.
Fadar ta ce Najeriya ta taɓa aiwatar da tsarin a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa amma bai cimma nasarar da ake so ba.

Source: Twitter
Babban mataimaki na musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan kafafen sada zumunta da sabbin kafafen yaɗa labarai, O’tega Ogra, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
An dura kan Atiku game da tallafi
Ogra ya ce ƙwarewar Najeriya wajen ba matatun mai na cikin gida tallafin samarwa a lokacin gwamnatin da Atiku ya yi mataimakin shugaban ƙasa ta haifar da sakamakon da ya kira “abin takaici matuƙa”.
Ya kawo bayanai da suka nuna cewa zuwa shekarar 2002, rabon ɗanyen mai na cikin gida da Hukumar Man Fetur ta Najeriya, NNPC, ke warewa ya kai ganga 445,000 a kowace rana, ana samar da shi ga matatun cikin gida bisa sharuddan rangwame.
A cewar Ogra, Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF, ya kiyasta kuɗaɗen shiga da aka rasa sakamakon tsarin da kashi 3.2 cikin 100 na GDP a 2002, da kashi 2.9 cikin 100 a 2003.

Kara karanta wannan
Hankalin Dangote ya tashi kan maido tallafin mai, Atiku ya masa bayani dalla dalla
Ya tambayi abin da ’yan Najeriya suka samu a madadin wannan tallafi, yana mai nuna raguwar amfani da matatun mai a lokacin.
Ogra ya yi nuni da alkaluman NNPC da suka nuna cewa amfani da matatar Warri ya kai kashi 14.27 cikin 100 a 2003, sannan kashi 9.10 cikin 100 a 2004.
Ya ce amfani da matatar Kaduna ya kai kashi 15.96 cikin 100 a 2003, sannan ya ƙaru zuwa kashi 26 cikin 100 a 2004.
Ogra ya ƙara da cewa amfani da matatar mai ta Port Harcourt ya ragu daga kashi 60.73 cikin 100 a 2001 zuwa kashi 31.04 cikin 100 a shekarar 2004.
Ya kuma ce tallafin bai hana ƙarin farashin fetur ba, yana zargin cewa farashin fetur ya ninka fiye da sau uku zuwa shekarar 2004, sannan ya kusan ninka sau huɗu kafin Atiku ya bar mulki.
Ogra ya kuma tuna cewa a ranar 9 ga Oktoba, 2003, gwamnatin ta soke rangwamen ta hanyar umarnin shugaban ƙasa PRES/158, inda tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya umarci NNPC ta biya cikakken farashin ɗanyen mai na duniya.
Ya ce:
“An gwada tallafin samarwarku, ya gaza kuma aka soke shi, alhali kana mataimakin shugaban ƙasa."
Mataimakin na shugaban ƙasar ya ƙalubalanci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya gabatar da hujjar cewa tsarin ya yi aiki a lokacin da aka fara aiwatar da shi.
Ya bayyana cewa tsohon shirin tallafin samarwa ya samar da attajirai, yana tambayar ko shawarar Atiku na yanzu na da nufin samar da irin waɗannan masu cin gajiyar shirin.
A ƙarshe, Ogra ya ce wa Atiku, “har yanzu wannan ita ce ka’idar da kuka aiwatar a wancan lokacin, kuma har yanzu ba mu sauya ƙasa ba,” yana mai cewa ƙasar tana da sakamakon gwajin da aka gudanar a baya.
Tinubu, Atiku sun kashe daloli a Amurka
Mun ba ku labarin cewa Bola Tinubu da Atiku Abubakar sun kashe miliyoyin dala wajen neman tasiri a Amurka, adadin da ya kai sama da N14bn a Najeriya.
Naira biliyan 14bdin da aka kashe wajen lobbying na iya tallafa wa kananan ‘yan kasuwa 56,000 idan aka ware N250,000 ga kowannensu.
Masana sun ce ya kamata a tantance amfanin kudin bin kafa, musamman ganin yadda ‘yan Najeriya ke fama da rashin aikin yi da matsalolin tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

