Dan Takara Ya Yi Alkawarin Rushe Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa idan Ya Ci Zaben 2027
- Ɗan takarar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba
- Sowore ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi irin wannan ofishi ba don haka zai rushe dhi idan ya ci zaben 2027
- Ya ce matakin ba zai shafi aurensa ba, amma matarsa ba za ta samu wani matsayi na hukuma a matsayin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria — Ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya ce ba zai amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ko ci gaba da tafiyar da shi ba idan ya zama shugaban Najeriya.
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba, yana mai cewa zama shugaban ƙasa ba zai shafi aurensa ba, domin hakan ba zai haifar da ƙirƙirar wani matsayi na hukuma ga matarsa ba.

Kara karanta wannan
Tun ba a je ko'ina ba shirin hada kan 'yan adawa don tunkarar Tinubu ya gamu da cikas

Source: Facebook
Sowore ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na Channels Television ranar Alhamis.
Sowore zai rusa ofishin matar shugavan kasa
A cewarsa, gwamnatinsa za ta gudanar da mulki ne bisa tanadin kundin tsarin mulki kawai, kuma ba za ta ci gaba da tafiyar da abin da ya bayyana a matsayin ofishi da kundin tsarin mulki bai tanada ba.
Dan takarar AAC ya ce:
“Za mu bi kundin tsarin mulki, kuma na karanta dukkan dokokin Najeriya, na da, da na yanzu, ciki har da kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi yanzu.
“Babu Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa a ciki, amma babu wanda zai iya soke aurena, ka san zama shugaban ƙasa ba zai soke aurena ba, amma ba zan yarda da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ba, ko shakka babu.”
Sowore na mayar da martani ne ga tambayar ko matarsa za ta dawo Najeriya domin ɗaukar matsayin Uwargidan Shugaban Ƙasa idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Farashin litar fetur na iya haura N5000 bayan zaben 2027, an gano dalili
Mata za su samu wakilci a mulkin Sowore
Sowore ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa rashin samun ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa zai hana mata samun damar bayyana ra’ayoyinsu a cikin gwamnatinsa.
A cewarsa, za a wakilci mata kuma za a saurari ra’ayoyinsu, amma ya tambayi dalilin ci gaba da tafiyar da wani ofishi da yake ganin kundin tsarin mulki bai tanada ba.

Source: Facebook
Ɗan takarar AAC ya kuma soki wasu daga cikin tsofaffin Uwargidan Shugaban Ƙasa, yana mai cewa ofishin bai kawo gagarumin sauyi ga matsayin mata a ƙasar ba.
“Mun samu Uwargidan Shugaban Ƙasa da dama, amma ba su kawo wani babban sauyi wajen inganta matsayin mata a ƙasar ba," in ji shi.
Sowore ya kammala da cewa rusa Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa zai kasance ɗaya daga cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi.
Sowore ya yi alkawarin albashin N500,000
Kun ji cewa Omoyele Sowore ya yi alkawarin kafa mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa a 2027.
Sowore, wanda ɗan gwagwarmaya ne, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin AAC za ta samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24.
Asali: Legit.ng