Tinubu Ya Jaddada Matsayarsa kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur

Tinubu Ya Jaddada Matsayarsa kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu shirin dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa hakan zai lalata gyare-gyaren da aka yi
  • Bayo Onanuga ya soki shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur, yana cewa zai jawo matsalolin kasafin kuɗi tare da hana zuba jari
  • Masana tattalin arziki sun ce kamata ya yi a mayar da hankali kan samarwa da inganta rayuwar ’yan Najeriya, ba tallafa wa amfani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta ce kiran tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur zai lalata gyare-gyaren da aka yi.

Fadar ta ce hakan zai kuma haifar da matsalolin doka da kasafin kuɗi, tare da yiwuwar rage sha’awar zuba jari a matatun mai.

Fadar shugaban kasa ta magangu kan cire tallafi a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a jerin saƙonnin da ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Maganar dawo da tallafi na taɓa Tinubu, ya tona wa Atiku 'asiri' kan matatun mai

Martanin fadar shugaban kasa ga Atiku

Sanarwar ta ce hakan na iya shafar matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai da ke cikin gida.

Onanuga yana mayar da martani ne kan shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya bayyana matakin a matsayin koma-baya, wanda ba zai dore ta fuskar kuɗaɗen gwamnati ba, tare da cewa ya samo asali ne daga “tsananin burin lashe shugabancin ƙasa”.

Onanuga ya ce harkar man fetur ta Najeriya ta sauya matuƙa tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur.

Ministan kudi ya kare maganar cire tallafin mai
Ministan kudi, Taiwo Oyedele yayin taro a Abuja. Hoto: Taiwo Oyedele.
Source: Facebook

Ministan kudi ya fadi kudin tallafi da aka samu

Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin ya samar da naira tiriliyan 15.8 ga tarayya tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta samu naira tiriliyan 5.4, yayin da aka raba naira tiriliyan 10.4 ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kira wa kansa ruwa bayan neman Atiku ya hakura da takara a 2027

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa kwanan nan.

Tinubu ya ce shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya nuna babban rashin fahimtarsa kan harkokin shugabanci da tattalin arziƙi.

Atiku, wanda ke daga cikin manyan masu neman shugabancin Najeriya, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur ne yayin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Matakin ya sa farashin man fetur a gidajen mai ya tashi daga ƙasa da naira 200 zuwa sama da naira 1,000, lamarin da ya ƙara tsadar sufuri da abinci.

Tinubu ya tafi kasar Faransa

An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya isa Paris, Faransa, domin ci gaba da hutun shekara na makonni uku da ya fara a Turai.

Bola Tinubu ya bar Abuja ranar 30 ga Agusta 2026, inda ya fara hutunsa a London kafin ya wuce Paris.

Tun bayan hawansa mulki, Tinubu ya ziyarci Faransa sau akalla 13, yayin da ya shafe sama da kwanaki 270 a ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.