Abu Ya Girma: Shugaba Tinubu Ya Dauki Zafi kan Mutuwar Matasa 37 a Ofishin Hukumar NSCDC
- Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gudanar da bincike na gaskiya kan mutuwar mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun NSCDC
- Tinubu ya ce babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya rasa ransa yana tsare a hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi ko rashin kula da aiki
- Shugaban ya umarci hukumomi su tabbatar da binciken ya kasance mai zurfi, a bayyane kuma ba tare da katsalandan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria — Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan mutuwar mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Neja.
Waɗanda ake zargin sun rasa rayukansu ne s dakin ajiyar masu laifi na Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) bayan an kama su a jihar Neja.

Source: Facebook
Leadeeship ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce ran kowane ɗan Najeriya yana da muhimmanci.
Shugaban kasar ya kuma ce bai kamata wani ɗan ƙasa ya rasa ransa yana hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi, rashin tausayi ko gazawar jami’i wajen sauke nauyin da ke kansa ba.
Tinubu ya nuna matuƙar damuwa kan rahoton mutuwar mutanen, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban batu da ke buƙatar bincike cikin gaggawa da ɗora alhakin da ya dace.
Tinubu ya buƙaci ɗaukar mataki
Shugaban ya ce:
"Yayin da Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da sauran ayyukan laifi a faɗin ƙasar, dole ne a gudanar da ayyukan tabbatar da doka bisa tanadin doka tare da cikakken mutunta haƙƙoƙin ɗan Adam na kowane mutum da ke tsare.
“Duk da ana zargin waɗannan mutane da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, suna da haƙƙin rayuwa, mutunci da kulawa irin ta ɗan Adam yayin da suke hannun gwamnati.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
"Gwamnati ba za ta amince da mutuwar mutane da yawa sakamakon sakacin jami’ai, gazawar sauke nauyi ko rashin kare rayukan mutanen da aka damƙa musu kulawa ba.
An bayyana abin da binciken zai ƙunsa
Tinubu ya umarci hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da cewa binciken ya kasance cikakke, a bayyane kuma ba tare da wani cikas ba.
Ya ce binciken ya kamata ya duba yadda aka kama mutanen, halin da waɗanda ake tsare da su suka shiga, yanayin wurin da aka tsare su, adadin da ke cikin wurin, irin kulawar lafiya da aka ba su da abubuwan da suka faru kafin mutuwarsu.

Source: Twitter
Ya umarci Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da hukumar NSCDC su ba dukkan hukumomin da ke gudanar da binciken cikakken haɗin kai, tare da tabbatar da cewa babu jami’in da zai yi katsalandan ko ƙoƙarin kawo cikas wajen gano gaskiyar lamarin.
Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da addu’ar Allah Ya jiƙan su.
Gwamnati ta dakatar da kwamandan NSCDC
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, baya1n mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan nan take tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Asali: Legit.ng
