"Abin da Zai Sa Tinubu Ya Tumurmusa Yan Adawa, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027"

"Abin da Zai Sa Tinubu Ya Tumurmusa Yan Adawa, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027"

  • Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya ce ba zai dora wa kawancen jam’iyyun adawa laifin rashin nasara ba idan Bola Tinubu ya lashe zaben 2027
  • Dalung ya ce zai amince da sake zaben Tinubu a matsayin hukuncin ’yan Najeriya idan shugaban kasar ya samu nasara a 2027
  • Jam’iyyun adawa shida sun gabatar da shirin kafa “gwamnatin kwarewar kasa” na wa’adin mika mulki na shekaru hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya ce idan Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zaben shugaban kasa a 2027, ba zai dora hakan kan gazawar kawancen jam’iyyun adawa na hada kai ba.

Tsohon ministan ya ce zai karbi nasarar Tinubu a matsayin zabin da ’yan Najeriya suka yi da hannayensu idan aka sake zaben shugaban kasar a 2027.

Kara karanta wannan

2027: Zulum ya ce mulki zai dawo Arewa, ya fadi lokaci

Solomon Dalung.
Tsohon ministan harkokin wasanni, Solomon Dalung yayin da yake hira da manema labarai Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

Dalung ya ce zai karbi zabin yan Najeriya

Dalung ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Television da aka watsa ranar Litinin.

“Zan karbe shi a matsayin hukuncin ’yan Najeriya. Hakan zai nuna cewa ba mu yi daidai da ’yan Najeriya ba kan batutuwan da suka shafi mulkin wannan kasa,” in ji shi.

Ya kara da cewa ba zai dora wa kawancen jam’iyyun adawa laifin hakan ba, domin kawancen yana magana ne a madadin al’ummar Najeriya, wadanda suke da ikon mallakar kasa da kuma ikon zabar wanda zai mulke su.

“Saboda haka, idan suka zabi Bola Tinubu a 2027, a matsayina na dan jam’iyyar dimokuradiyya, zan karbe shi a matsayin hukuncin al’umma,” in ji Dalung.

Jam’iyyun adawa na shirin hada kai

Kalaman Dalung sun zo ne makonni biyu bayan jam’iyyun adawa shida sun gabatar da shawarar kafa “gwamnatin kwarewar kasa” wadda za ta yi mulki na tsawon wa’adi guda na shekaru hudu gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

An gindaya wa Nyesom Wike sharuɗa 2 game da APC kafin zaben 2027

An gabatar da shawarar ne a wani taron kolin jam’iyyun siyasar adawa da kungiyar G100 ta shirya a Abuja.

Jam’iyyun da suka samu wakilci a taron sun hada da ADC, APM, NDC, PDP, PRP) da kuma SDP.

Salihu Lukman, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, ne ya gabatar da shawarar a taron.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya karbi bakuncin wasu mutane a Fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya ce shirin gwamnatin da aka gabatar zai dogara ne kan ka’idoji guda hudu: kwarewa, gaskiya, hada kan kasa da kuma wakilci na adalci, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Jam’iyyun adawar sun kuma gabatar da shawarar samar da yarjejeniyar mika mulki da za a iya aiwatar da ita ta hanyar doka domin tabbatar da cewa jam’iyyun da suka shiga kawancen sun mutunta yarjejeniyar.

Solomon Dalung ya ce ba zai dora wa laifi ba idan suka sha kaye a zaben 2027, yana mai cewa duk wanda ya samu nasara shi ne zabin yan Najeriya.

Hada kan yan adawa na fuskantar matsala

Kun ji cewa, yunkurin kungiyar G-100 na tsayar da dan takarar shugaban kasa guda daya na jam'iyyun adawa na fuskantar sabon kalubale.

Hakan dai ya biyo bayan alamun da aka gani daga bangarorin Atiku Abubakar, Peter Obi da Gwamna Seyi Makinde, wadanda suka nuna ba za su janye daga takara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262