An Hango Abin da Zai Faru idan Atiku Obi da Suka Hade don Tunkarar Tinubu a 2027
- Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, ya yi hasashen cewa Bola Tinubu zai samu sama da ƙuri’u miliyan 12 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Fayose ya ce Tinubu zai iya doke Atiku Abubakar da Peter Obi ko da sun haɗa kai domin tsayawa takara tare
- Tsohon gwamnan ya bayyana Tinubu a matsayin hanyar da ta fi kusa wajen mayar da mulkin shugaban ƙasa zuwa Arewa bayan wa’adin mulkin Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi hasashen nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Ayo Fayose ce yana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai samu sama da ƙuri’u miliyan 12 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Twitter
Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Tv da aka watsa ranar Talata, 15 ga watan Satumban 2026.
Fayose ya ce Tinubu zai doke Atiku da Obi
Tsohon gwamnan ya ce Tinubu zai iya doke Atiku Abubakar, ɗan takarar African Democratic Congress (ADC), da Peter Obi, ɗan takarar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Ya ce hakan zai faru ko da Atiku da Obi sun haɗa kai domin fuskantar Tinubu a zaɓen.
“Wannan takara ce tsakanin mutane uku; watakila ban faɗa ta yadda ya kamata ba. Atiku yana nan, Obi yana nan. Ko da sun haɗa kai, wannan mutumin (Tinubu) zai yi nasara a kansu,” in ji Fayose.
Ya ce idan Atiku da Obi suka yi takara daban-daban, ƙuri’unsu za su rabu, abin da zai ƙara tasiri kan sakamakon zaɓen.
Ya ce Kudu maso Yamma za ta taimaka wa Tinubu
Fayose ya yi iƙirarin cewa Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a jihohin Kudu maso Yamma.
Ya ce Tinubu zai samu nasara da bambancin ƙuri’u tsakanin miliyan biyar zuwa shida a yankin, yana tambayar irin tsarin da Atiku ko Obi ke da shi a jihohin Ekiti, Osun da Ondo.
“Wannan siyasar ba wasan shan shayi ba ce. Asiwaju zai samu sama da ƙuri’u miliyan 12. Yin magudin zaɓe a yanzu ya yi matuƙar wahala,” in ji shi.
Fayose na son mulki ya ci gaba da zama a Kudu
Fayose ya kuma ce a ganinsa, ya kamata mulki ya kasance a Kudu na tsawon shekaru takwas, sannan Tinubu ya zama hanyar da ta fi kusa wajen mayar da mulkin zuwa Arewa.
Ya ce idan Atiku ya samu mulki, zai iya neman ya shafe shekaru takwas, haka ma idan Peter Obi ya samu nasara.
“Bola Ahmed Tinubu shi ne hanya mafi kusa wajen mayar da mulki Arewa. Duk wani ɗan Arewa da ke takara a yanzu, a ganina, yana takara ne kawai,” in ji shi.

Source: Facebook
Peter Obi ya bukaci a saki takardun karatunsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya nemi Jami’ar UNN da ke Nsukka ta fitar da takardun karatunsa.
Ya ce ba shi da wata matsala da a fitar da takardun digirinsa da sauran bayanan da suka shafi karatunsa a jami’ar.
Asali: Legit.ng

