Abin da Ya Sa Malaman jami’a 600 a Arewa Suke Goyon Bayan Tazarcen Tinubu

Abin da Ya Sa Malaman jami’a 600 a Arewa Suke Goyon Bayan Tazarcen Tinubu

  • Malaman jami’a sama da 600 ne suka duba alkaluma, suka yanke shawarar goyon bayan Bola Tinubu a 2027
  • Shugaban jami’ar KASU ya sun samu tallafin fiye da N1bn daga NELFUND ban da daukar nauyin wasu ayyuka
  • Farfesa Abdullahi Musa ya ce nasarorin da APC ta samu a kan mulki ya sa suka ga bukatar su mara mata baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Shugaban jami’ar jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Musa, ya yi magana a game da matakin da suka dauka a siyasance.

A farkon makon nan aka ji yana sanar da duniya cewa malamai 600 daga jami’o’i na jihohin Arewa suna tare da Bola Tinubu.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu bayan sake samun takara a APC Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban jami'ar KASU ya yi karin haske

Ranar Talata, Tashar Trust TV ta zanta da malamin jami’ar domin jin meyasa shi da abokan aikinsa suke goyon bayan APC a 2027.

Kara karanta wannan

‘Yan Boko Haram sun yi sabon bidiyo da ya yi maganar batun sulhu da Gwamnatin Tarayya

Farfesa Abdullahi Musa ya ce sun yi na’am da tazarcen shugaba Tinubu ne duba da ayyukan da gwamnatinsa ta kawo.

Da farko ‘dan jarida ya fara tambayar shi a kan taron da suka yi, ko suna da masaniya an kira su ne domin manufar siyasa.

Farfesan ya nuna cewa ba a fito karara an shaida masu cewa za su zo wurin ne domin su goyi bayan tikitin Tinubu/Shettima ba.

Meyasa malaman jami'a suka bi Bola Tinubu?

Sai dai bayan nazarin kokarin da gwamnati mai-ci ta yi, shugaban jami’ar ya ce malaman sun ga bukatar a bi bayan APC a 2027.

Abdullahi Musa ya ce sun duba cigaban da aka kawo a fannin ilmi, abubuwan more rayuwa da harkar noma kafin su yi maganar.

Shugaban jami’ar ya shaida wa gidan talabijin cewa asali an yi zaman ne da nufin a ba da shawarar matakin da za a dauka a 2027.

Kara karanta wannan

Shehu Buba: ‘Dan takarar gwamna da ake zargi da ta’addanci ya kai kan shi wajen hukuma

"Abin da taron ya nuna shi ne wani dandali ne da malamai za su hadu, su duba wasu bayanai, su yi nazarinsu daga nan sai su yi amfani da tsari na bincike domin bada shawarar mataki na gaba da za a dauka."

- Farfesa Abdullahi Musa

Jami'ar KASU ta amfana da NELFUND & TETFund

Don haka ne masanan suka yi nazarin ayyukan da gwamnatin Tinubu ta yi a shekaru uku, ta ga dacewar ta zarce a Mayun 2027.

Vanguard ta rahoto shi yana bada misali da hobbasar da aka yi a bangaren ilmi a sanadiyyar fito da tsarin nan na NELFUND.

Farfesa Musa ya ce daliban jami’arsa kawai sun samu tallafin N1bn daga tsarin domin su yi karatu.

Baya ga haka ya ce sun samu gudumuwa sosai daga hukumar TETFund da Hukumar kula da harkar wasanni a jami’ar ta KASU.

A karshe farfesan ya ce malaman jami’ar suna da damar ayyana ra’ayinsu a siyasance kamar kowa.

Wani malami a fannin aikin jarida a jami'ar ABU Zariya, Dr. Muhammad Hashim Sulaiman ya wallafa hirar a shafinsa na Facebook.

ADC ta soki ra'ayin malaman jami'a

Ana da labari ADC ta nuna rashin amincewa da matakin da malaman jami’a suka dauka na fito kararar su bi bayan Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Jam'iyyar adawar bukaci INEC kar ta yi amfani da wadannan malamai a zaben 2027 kamar yadda aka saba tun a shekarar 2011.

Duk da kowa yana da ra’ayinsa, wasu na ganin tunda ana zaben malaman jami’a su yi aiki lokacin zabe, bai kamata su kama layi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng