2027: Sabon Rikici Ya Barke tsakanin Wike da Gwamnonin APC
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da matsayar gwamnonin APC da ke neman masu goyon bayan Bola Tinubu su marawa ‘yan takarar jam’iyyar baya
- Wike, wanda har yanzu mamba ne a PDP, ya ce goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba yana nufin zai goyi bayan ‘yan takarar APC ba ne
- Ministan ya bayyana wasu daga cikin gwamnonin da suka gabatar da matsayar a matsayin ‘yan siyasa masu kasala, yana mai cewa suna da 'yancin yin hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya mayar da martani kan matsayar Gwamnonin APC game da masu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Wike ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu ba ya tilasta masa ko wasu ’yan siyasa su goyi bayan ‘yan takarar APC a zaɓen gwamna, Majalisar Tarayya ko sauran kujeru.

Source: Twitter
Wike ya soki gwamnonin APC
The Sun ta rahoto cewa Wike ya bayyana matsayar gwamnonin a matsayin wata magana da aka yi saboda dalilan siyasa, yana mai cewa wasu daga cikin wadanda suka gabatar da ita ba su da kwarewa a siyasa.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce zaɓen 2023 ya nuna cewa masu kaɗa ƙuri’a na iya zaɓar ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban a rana guda.
Ya tambayi ko goyon bayan Tinubu da wasu ’yan siyasa (Kamar shi) ke yi yana nufin ba za su iya goyon bayan ‘yan takara a sauran zaɓuka ba.
“Goyon bayana ga Tinubu ne kawai”
Wike ya ce bai taɓa ɓoye matsayarsa ta goyon bayan Tinubu ba, yana mai cewa ra’ayinsa ya samo asali ne daga fahimtarsa cewa ya kamata shugabancin Najeriya ya ci gaba da kasancewa a Kudancin ƙasar.
Punch ta wallafa cewa ya ce goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa ba yana nufin ya bar jam’iyyarsa ko ya daina goyon bayan ‘yan takarar wasu jam’iyyu a sauran matakan zaɓe ba.
“Na taɓa ɓoye cewa zan goyi bayan Shugaban ƙasa? Ban taɓa ɓoye hakan ba. Dangane da shugabancin ƙasa, za mu goyi bayansa saboda na yi imanin cewa shugabancin ƙasa ya kamata ya ci gaba da kasancewa a Kudu,”
In ji shi.
Wike ya kuma ce batun gwamnonin ya fi shafar bukatunsu na siyasa da tsarin jam’iyyarsu fiye da batun sake zaɓen Tinubu.
Matsayar Wike a siyasar 2027
Wike ya ce Shugaba Tinubu ya san irin ayyukan siyasar da yake yi, kuma bai taɓa ɓoye masa matsayinsa ba.
Ya kuma ƙi amincewa da ra’ayin cewa kasancewarsa a PDP yayin da yake goyon bayan Tinubu ya nuna rashin tabbas kan matsayinsa na siyasa.

Source: Facebook
Ministan ya ce a kodayaushe yana bayyana matsayinsa a fili, kuma goyon bayan shugaban ƙasa ba ya tilasta masa ya bar asalin jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan
'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'
Wike ya ƙara da cewa shugabanci nagari ya ƙunshi iya tafiyar da bambance-bambancen siyasa da haɗa mutane masu ra’ayoyi daban-daban.
Martanin gwamnonin APC
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnonin APC, karkashin jagorancin Hope Uzodimma, sun bayyana cewa ba za su shiga ko goyi bayan wani ƙawance ko tsarin siyasa da zai iya raunana APC ba.
Uzodimma ya bayyana matsayar ne bayan wata ganawar sirri da gwamnonin suka yi a Abuja, inda suka ce tsarin kamfen ɗinsu zai kasance ga ‘yan takarar APC a dukkan matakan zaɓen 2027.
Wannan matsaya ta zo ne a daidai lokacin da ake samun bambance-bambancen siyasa tsakanin Wike da wasu daga cikin gwamnonin APC, ciki har da Uzodimma da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Legit.ng

