Ko da Tsiya Tsiya: ADC Ta Bayyana Shirinta kan Zaben 2027
- ADC ta ce tana da cikakken yaƙinin cewa za ta kayar da APC a zaɓen 2027 idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci
- Jam’iyyar ta ce ta shirya kare ƙuri’un magoya bayanta, tana zargin APC da shirin yin amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen tasiri kan zaɓe
- Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya kuma yi tsokaci kan kalaman Nyesom Wike game da zaɓen gwamnan Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ta shirya fuskantar duk wani yanayi a zaɓen 2027 da ake tunkara.
ADC ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar kayar da jam’iyyar APC mai mulki idan aka gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce sakataren yaɗa labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Naija Unfiltered Podcast.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
A yayin hirar an tambaye shi ko ADC za ta iya kayar da jam’iyyar da ke kan mulki duk da yawan ƙungiyoyin adawa da ke neman shiga zaɓen 2027.
ADC ta ce ba ta shakka kan nasararta
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ba ta da shakka kan damar da take da ita ta samun nasara a zaɓen, sai dai ya nuna damuwa kan sahihancin tsarin zaɓen.
Ya ce idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, ADC na da tabbacin cewa za ta samu nasara.
“Eh, mun yi imanin haka. Idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, ba ni da ko shakka a raina cewa za mu lashe wannan zaɓe,” in ji shi.
Jam’iyyar ta ce za ka kare kuri’unta
Kakakin ADC ya ce jam’iyyar ta shirya kare ƙuri’un da magoya bayanta za su kada mata a zaɓen 2027.
Ya kuma zargi APC da shirin yin amfani da wasu hanyoyi wajen karkatar da sakamakon zaɓen, ko da yake bai gabatar da wata hujja a cikin hirar ba.
“Kalubalen shi ne: Shin za a samu zaɓe na gaskiya da adalci? Mun shirya hakan. Mun shirya fuskantar komai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta sanya ido sosai kan ƙuri’un da aka kada mata domin tabbatar da an kare su.
Kakakin ADC ya ambaci Wike da zaɓen Osun
Kakakin na ADC ya kuma yi tsokaci kan wani kalami da aka danganta ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, game da sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Bolaji Abdullahi ya ce kalaman Wike, na cewa da yana jihar Osun zai iya tabbatar da nasarar APC, sun haifar da tambayoyi game da yadda ministan da jam’iyyarsa za su iya yin tasiri kan sakamakon zaɓe.
“Me hakan yake nufi? Cewa ba tare da la’akari da abin da mutanen Osun suke tunani ba, kuna da hanyar tabbatar da sakamakon yadda kuke so. Wannan ikirari ne,” in ji shi.
ADC ta zargi APC da barazana
Bolaji Abdullahi ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da komawa ga yin barazana saboda, a cewarsa, ta rasa goyon bayan ’yan Najeriya.
Ya ce jam’iyyar ta san cewa ’yan Najeriya sun juya mata baya, shi ya sa ake ganin irin waɗannan barazanar.
Kakakin ADC ya ce saboda haka jam’iyyar na shirin shiga zaɓen 2027 da cikakken shiri, musamman wajen tabbatar da cewa an kare ƙuri’un magoya bayanta tun daga lokacin kada kuri’a har zuwa bayyana sakamako.

Source: Facebook
ADC ta fusata kan fatattakar mambobinta
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi kakkausan gargadi bayan ta yi zargin cewa an kai hari kan wasu daga cikin mambobinta a jihar Kaduna.
Jam'iyyar ta ce tashin hankalin da aka fara shigo da shi cikin harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027 na iya haifar da mummunan sakamako.
Asali: Legit.ng

