Daga Fara Kamfen, Manyan Magoya bayan Tinubu Suna Rikici a tsakaninsu
- Ƙawancen siyasa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke kira Rainbow Coalition ya jawo sabon sabani da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar APC
- Gwamnonin APC sun ce ba za su goyi bayan wani ƙawance da zai raunana jam’iyyar ko ta shafi ‘yan takararta a zaɓen 2027 ba
- Wike kuwa ya ce goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa ba yana nufin ya goyi bayan ‘yan takarar APC a sauran zaɓuka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ƙawancen siyasa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta a ƙarƙashin tsarin Rainbow Coalition ya jawo sabani da Gwamnonin APC gabanin zaɓen 2027.
Matsayar bangarorin biyu ta shafi yadda za a tsara goyon bayan da ake bai wa Tinubu, da kuma makomar ‘yan takarar APC a zaɓukan gwamna da na majalisun dokoki.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya kawo sabon tsarin tallafi da zai taimaki 'yan Najeriya

Source: Twitter
'Yan APC sun yi watsi da ƙawancen
Punch ta wallafa cewa ƙungiyar gwamnonin APC, ta bayyana cewa ba za ta shiga ko goyi bayan wata ƙawance da za ta raunana APC ko ta shafi damar ‘yan takarar jam’iyyar ba.
Shugaban ƙungiyar, Hope Uzodimma, ya bayyana matsayar ne bayan wata ganawar sirri da gwamnonin APC suka yi a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnonin sun ce za su yi aiki tare wajen kare muradun jam’iyyar da ‘yan takararta a zaɓen 2027.
Martanin Nyesom Wike
Wike kuwa ya yi watsi da ra’ayin cewa Rainbow Coalition na aiki ne a kan wasu 'yan APC ko gwamnoninta da ke takara a jihohi.
Ya ce goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba ya nufin dole ne jam’iyyun da ke cikin ƙawancen su daina gabatar da ‘yan takara a sauran zaɓuka.
A wata hira da Arise TV, Wike ya bayyana cewa goyon bayansa ga Tinubu abu ne da ba zai sauya ba, amma ya ce hakan ba ya nufin ya bar PDP ko ya goyi bayan APC a dukkan matakan zaɓe.

Kara karanta wannan
'Yan kabilar Igbo sun yi watsi da Peter Obi sun bayyana dan takararsu a zaben 2027
Sabani ya shafi wasu jihohi
Rahoton the Guardian ya nuna cewa sabon yanayin siyasar ya kuma haifar da ce-ce-ku-ce a wasu jihohi, ciki har da Rivers da Kwara.
A Rivers, Wike ya bayyana cewa Rainbow Coalition za ta taka rawa wajen yanke wanda zai zama ɗan takararta na gwamna a 2027, yayin da ƙawancen ya ƙunshi ‘yan siyasa daga PDP da APC.
Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers ma ya bayyana goyon bayansa ga ƙawancen Wike tare da nuna goyon baya ga Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
A gefe guda, jam’iyyar APC ta nuna damuwa kan yadda sabanin Wike da wasu gwamnoninta zai iya shafar haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓen.
Gargadin shugaban APC
Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ta bakin mai magana da yawunsa, Abimbola Tooki, ya bayyana damuwa kan sabanin da ke tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC.
Ya ce jam’iyyar na son a tabbatar da cewa irin wannan rashin jituwa ba zai haifar da rarrabuwar kawuna da za ta shafi shirye-shiryen APC gabanin zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan
Magana ta kare, INEC ta fitar da sunayen yan takarar shugaban ƙasa na ƙarshe kafin zaben 2027
PDP kuwa ta bayyana cewa goyon bayan Wike ga Tinubu ba ya nufin ya bar jam’iyyarsa ko ya daina hulɗa da tsarin siyasar PDP.
Sabon sabanin ya sa batun Rainbow Coalition ya koma kan yadda za a tsara goyon bayan Tinubu tare da kare muradun APC da ‘yan takararta a sauran zaɓuka.
Hasashe kan zaben 2027
A wani labari, kun ji cewa Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi hasashen sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya ce Bola Tinubu zai zo na 1, Atiku Abubakar na 2, yayin da Peter Obi zai zo na 3.
Afegbua ya bayyana hakan ne yayin da yake nazarin damar manyan ‘yan takarar adawa a wata hira, inda ya ce gasar za ta fi karkata tsakanin waɗannan ‘yan siyasa uku.
Ya kuma yi tambaya kan damar Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da kuma ɗan takarar AAC, Omoyele Sowore, yana mai bayyana na biyun a matsayin ‘yan siyasar da ke yawan hayaniya.
Asali: Legit.ng