Dalibar da Ta Lashe Gasar Alƙur'ani Ta Duniya Ta Samu Kyauta Mai Tsoka daga Matar Tinubu

Dalibar da Ta Lashe Gasar Alƙur'ani Ta Duniya Ta Samu Kyauta Mai Tsoka daga Matar Tinubu

  • Uwargidan Shugaban Ƙasa ta yaba wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi bayan ta lashe Gasar Alƙur’ani ta Sarki Abdulaziz karo na 46 a Makkah, Saudi Arabia
  • Sanata Oluremi Tinubu ta ba Maryam kyautar N20m tare da bayyana nasarar ta a matsayin abin alfahari ga Najeriya da ’ya’ya mata
  • Gwamna Inuwa Yahaya da iyalan Maryam sun yaba wa Uwargidan Shugaban Ƙasa kan girmama nasarar da ta samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta yaba wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi bisa nasarar da ta samu a Gasar Alƙur’ani ta duniya ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Makkah, Saudi Arabia.

Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne ranar Talata, 15 ga watan Satumba, 2026 a Abuja, inda ta kuma ba Maryam kyautar Naira miliyan 20.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tura tawagar gwamnoni gidan Sheikh Jingir ta'aziyya

Maryam Dan Azumi.
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu lokacin da ta karbi bakuncin Maryam ibrahim Dan'azu da mahaifinsa da tawagar gwamnan jihar Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnn jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya ne ya jagoranci Maryam zuwa wurin uwargidan Shugaba Tinubu, tare fa takiyar mahaifinta, Ibrahim Dan’Azumi.

Oluremi ta yaba da nasarar Maryam

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana nasarar Maryam a matsayin abin alfahari ga Najeriya da kuma ’ya’ya mata a faɗin duniya.

Ta ce Maryam ta zama abin koyi ga ’ya’ya mata, tare da yaba wa iyayenta saboda yadda suka tallafa mata wajen karatunta tare da bunƙasa baiwar da take da ita.

Oluremi ta ce nasarar ba ta tsaya kan samun nasara ta mutum ɗaya ba, domin ta zama abin alfahari ga ƙasa, yayin da Maryam ta ɗaukaka Najeriya a matakin duniya ta hanyar ƙwarewarta wajen karatun Alƙur’ani Mai Girma.

Matar Tinubu ya jinjinawa iyayen Maryam

Ta kuma bayyana Maryam da babbar yayarta, Hajara, wadda ta zo ta farko a wata irin wannan gasa da aka gudanar a Jordan a shekarar 2024, a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu

Matar Tinubu ta kuma yaba wa iyayensu, malamai da masu horar da su, da kuma Gwamna Inuwa Yahaya bisa jagoranci da tallafin da suka ba su.

“Nasarar Maryam ta nuna muhimmancin aiki tuƙuru, ladabtar da kai da kuma jajircewa. Ina ƙarfafa ta da ta rungumi samun jagoranci da shawarwari daga masu ƙwarewa yayin da take ci gaba da karatunta,” in ji Oluremi Tinubu.

Maryam ta gode wa Oluremi Tinubu

Da take mayar da martani, Maryam Dan’Azumi ta gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa bisa karrama ta.

Ta ce shiga gasar da aka gudanar a Saudi Arabia ya ba ta damar samun ƙarin gogewa da bayyana kanta a matakin duniya.

Remi da Maryam.
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu tare da gwarzuwaar gsar Alkur'ani ta duniya, Maryam Ibrahim Dan'Azumi Hoto: Muhammed Inuwa Yahaya
Source: Facebook

Ta bayyana fatan cewa nasarar da ta samu za ta ƙarfafa sauran matasan Najeriya su ƙara himma wajen neman nasara.

Maryam Dan’Azumi ta kuma nuna farin ciki, inda cikin murna ta miƙa kyautar da ta samu a wurin gasar Alkur'sni ga Uwargidan Shugaban Ƙasa.

Matar Tinubu ta roki yan Najeriya

Kun ji cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta roƙi ’yan Kudu maso Gabas su sake zaɓar mijinta, Bola Tinubu, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Oluremi Tinubu ta ce tana son ganin Najeriya ta inganta kafin ta tsufa, yayin da ta bayyana cewa ita da shugaban ƙasa suna aiki don cigaban ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262