Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban Kasa Gidan Yari kan Aikata Laifuffukan Yaki

Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban Kasa Gidan Yari kan Aikata Laifuffukan Yaki

  • Kotun laifukan yaki na Kosovo ta yanke wa tsohon shugaban Kosovo, Hashim Thaci, hukuncin shekaru 25 a gidan yari saboda laifukan yaƙi
  • An same shi da hannu wajen kisan mutane 96, tsare mutane 385 ba bisa ƙa’ida ba, azabtar da 303 da kuma wulakanta kusan 50
  • Tsoffin kwamandojin KLA uku da aka gurfanar tare da Thaci su ma sun samu hukunci, yayin da aka wanke su daga wasu tuhume-tuhume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Hague - An yanke wa tsohon shugaban Kosovo, Hashim Thaci, hukuncin shekaru 25 a gidan yari bayan wata kotu da ke Hague ta same shi da alhakin aikata laifukan yaƙi.

Thaci, mai shekaru 58, an same shi da laifukan kisa, azabtarwa, wulakanci da kuma tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba.

A yankewa Hashim Thaci hukunci
Tsohon shugaban kasar Kosovo, Hashim Thaci Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Tashar Sky News ta ce laifukan sun faru ne a lokacin da yake babban kwamandan Kosovo Liberation Army (KLA), ƙungiyar ’yan Albaniya da ke fafutukar ballewar Kosovo daga Serbia a shekarun 1990.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

An same shi da hannu wajen kisan mutane 96

Kwamitin alkalai ya ce dakarun KLA sun kashe mutane 96 da ake zargi da adawa da ƙungiyar ko kuma haɗin gwiwa da jami’an tsaron Serbia.

Kotun ta kuma same Thaci da alhakin tsare mutane 385 ba bisa ƙa’ida ba, azabtar da 303, da kuma mummunan mu’amala da kusan 50.

Alƙalin da ya jagoranci shari’ar, Charles Smith, ya ce Thaci ya “shiga cikin aikata laifukan tare da ƙarfafa su”.

Ya ce girma da kuma yanayin laifukan da aka aikata suna da matuƙar muni.

Kotun ta ce an kama mutane bisa jita-jita

Alƙalin ya ce wasu daga cikin bayanan sirrin da aka yi amfani da su wajen kamu, tsarewa da kuma kashe waɗanda abin ya shafa ba su wuce jita-jitar da ba a tabbatar da ita ba.

Ya ce an kira wasu daga cikin waɗanda aka tsare da sunayen ’yan leƙen asiri ko masu haɗin gwiwa, sannan aka yi musu mugun abu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000

Smith, wanda ɗan ƙasar Amurka ne, ya jaddada cewa shari’ar ba ta shafi halaccin KLA ko kuma burinta na samun ’yancin kai ga Kosovo ba.

An yankewa tsofaffin kwamandojin KLA hukunci

Hashim Thaci ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Ya tsaya ya yi shiru yayin da aka karanta masa hukuncin. An ba shi damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

An gurfanar da shi tare da wasu tsofaffin manyan kwamandojin KLA uku, wato Kadri Veseli, Rexhep Selimi da Jakup Krasniqi, kan laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama.

Masu gabatar da ƙara sun nemi a yanke wa Thaci da sauran waɗanda ake tuhuma hukuncin mafi ƙarancin shekaru 45 a gidan yari.

Sai dai kotun ta yanke wa Veseli shekaru 18, Selimi shekaru 13, yayin da aka yanke wa Krasniqi shekaru 25.

Thaci ya samu hukunci
Hashim Thaci, tsohon shugaban kasar Kosovo Hoto: Ferdi Limani
Source: Getty Images

An wanke su daga wasu tuhume-tuhume

Kotun ta wanke mutanen huɗun daga tuhume-tuhume guda shida da suka shafi laifukan cin zarafin bil’adama.

Alƙalai sun ce masu gabatar da ƙara ba su iya tabbatar da cewa an aikata waɗannan laifukan ne a matsayin wani ɓangare na farmaki mai faɗi da tsari kan fararen hula ba.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, gagarumar matsala ta tunkaro hukumar INEC

Kotu ta kwace N150m na dan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace Naira miliyan 150 da ake dangantawa da dan majalisar wakilai, Nicholas Mutu.

Alkalin kotun, mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin ne bayan ta amince da bukatar EFCC na kwace kudin har abada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng