'Yan Bindiga Sun Yi wa Mace Mai Ciki da Jariri Ta'addanci a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi wa Mace Mai Ciki da Jariri Ta'addanci a Kaduna

  • ’Yan bindiga sun kai hari wani gida a Kaduna, inda suka yi awon gaba da wata mai juna biyu, wani mutum da matarsa da kuma jaririnsu dan wata shida
  • Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin a Alrahus da ke Millennium City, Chikun a Jihar Kaduna, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici
  • Mijin mata mai juna biyun ya ce masu garkuwar sun tuntube shi daga bisani tare da neman makudan kuɗin fansa domin sakin matarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – ’Yan bindiga sun kai hari yankin Estate da ke Millennium City a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutum huɗu.

Mutanen da aka sace sun haɗa da wata mai juna biyu, wani mutum da matarsa da kuma jaririnsu mai wata shida.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta rahoto cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, inda maharan suka rika shiga gidaje suna neman mutanen da za su yi garkuwa da su.

An nemi taimakon sojoji

Mijin matar mai juna biyu, Abdulladir Bello, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce yana Abuja lokacin da matarsa ta kira shi ta sanar da shi cewa wasu mutane na ƙoƙarin tilasta shiga harabar gidansu.

Ya ce ya yi ƙoƙarin kiran ’yan sanda domin neman taimako, amma bai samu damar hakan ba, lamarin da ya sa ya tuntubi sojoji.

“Na kasance a Abuja lokacin da ta kira ni da misalin ƙarfe 11:30 na dare ta ce ɓarayi suna ƙoƙarin tilasta shiga harabar gidanmu.
“Saboda na ruɗe, sai na yi ƙoƙarin kiran ’yan sanda, amma layukansu ba sa shiga. Daga nan sai na tuntubi sojoji, suka tura jami’ansu,”

In ji shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

An sace mutane huɗu a harin

Bello ya ce maharan sun tsere da matarsa mai juna biyu bayan sun shiga wani gidan da ke makwabtaka da nasu, inda suka yi garkuwa da wani mutum, matarsa da jaririnsu mai watanni shida.

Ya ƙara da cewa daga baya masu garkuwar sun tuntube shi tare da neman makudan kuɗin fansa domin sakin matarsa.

Bello ya yaba da yadda sojoji suka gaggauta kai ɗauki, tare da kira ga mazauna yankin da su ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna a ofis. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Harin ya sake tayar da hankali

Wani mazaunin yankin wanda aka kai wa gidansa hari, amma ya samu tserewa tare da iyalansa, ya ce maharan sun shiga wasu gidaje suna neman mutanen da za su sace.

Mazaunin, wanda ya ce ya koma wajen ne kimanin shekaru huɗu da suka gabata bayan ’yan bindiga sun addabi yankin Keke B da yake zaune a baya, ya ce sabon harin ya sake jefa mazauna cikin fargaba.

Kara karanta wannan

Kaico: Yan bindiga sun kashe basarake a yanayi mai ban tausayi a jihar Kano

Har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, ba a samu martanin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan ba, saboda ba a iya samun layinsa ta waya ba.

An kama gurgu a Kwara

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta kama wani gurgu mai shekaru 30, Umaru M., bayan an gano bindigogin AK-47 guda biyu.

Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce an kama mutumin ne yayin wani samame na binciken abubuwan hawa da jami’an tsaro suka gudanar a kan hanyar Alapa–Okolowo da ke Ilorin.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya fara musanta mallakar makamai, amma daga baya bincike ya sa ya amsa cewa yana jigilar makaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng