Tana Sama Tana Dabo kan Shirin Kirkirar Wasu Jihohi, Gwamna Ya Hango Matsala

Tana Sama Tana Dabo kan Shirin Kirkirar Wasu Jihohi, Gwamna Ya Hango Matsala

  • Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ba da shawara ga Gwamnatin Tarayya kan shirin kirkirar sababbin jihohi
  • Lawal ya ce matsalolin kudi da jihohin Najeriya 36 ke fuskanta sun sanya bukatar karin jihohi zama abin da ya kamata a sake tunani
  • Gwamnan ya ce Zamfara ta samu ci gaba tun bayan kirkirarta, musamman wajen aikin yi, bunkasar birane da noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya tura bukatata musamman ga Gwamnatin Tarayya kan shirin kirkirar sababbin jihohi.

Gwamna Dauda Lawal ya bukaci ta dakatar da kirkirar karin jihohi, yana mai cewa a fara karfafa wadanda ake da su.

Gwamna ya bukaci dakatar da shirin samar da wasu jihohi
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Lawal ya bayyana haka ne a Gusau yayin wata ganawa da shugabannin kafafen yada labarai, cikin shirye-shiryen bikin cikar Zamfara shekaru 30 da kafuwa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

An kirkiri Zamfara daga tsohuwar Jihar Sokoto a watan Oktoban 1996, lokacin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha, tare da Gusau matsayin babban birni.

Tun bayan kirkirarta, jihar ta gina nata tsarin gudanarwa da tattalin arziki, inda noma da albarkatun ma’adinai suke daga cikin manyan hanyoyin samun kudinta.

Dalilin gwamnan na ba da shawara

Sai dai Lawal ya ce yanayin da kasar ke ciki yanzu ya bambanta da lokacin da aka kirkiri Zamfara shekaru uku da suka gabata.

Ya ce matsalolin kudi da ke addabar jihohin Najeriya 36 sun sanya bukatar karin jihohi zama abin da ya kamata a sake nazari.

Ya ce:

“Bayan mun fahimci matsalolin kudi, hatta jihohin da aka riga aka kirkira yanzu suna fuskantar wahalar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.”

Gwamnan ya amince cewa kirkirar jihohi a baya ya taimaka wajen kusantar da gwamnati ga al’umma, tare da samar da ayyukan yi da bunkasar birane.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub ya rasu

Sai dai ya ce dole ne a fara magance matsalar dorewar jihohin da ake da su kafin a nemi kirkirar wasu sababbi, cewar Punch.

Gwamnan ya ce:

“Saboda haka, ina ganin ya kamata mu yi tunani sosai kafin mu fara neman kirkirar karin jihohi.”
Gwamna Dauda Lawal ya ba gwamnatin tarayya shawara
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Twitter

Yadda ake kirkirar sabuwar jiha

Matsayar gwamnan ta zo ne yayin da ake gudanar da bitar kundin tsarin mulki, inda bukatar kirkirar sabbin jihohi ta kasance cikin manyan batutuwan tattaunawa.

A karkashin sashe na takwas na kundin tsarin mulkin 1999, kirkirar jiha na bukatar matakai da dama, ciki har da goyon bayan ‘yan majalisun tarayya da jihohi.

Haka kuma, majalisun kananan hukumomi da kuri’ar jin ra’ayin jama’a suna daga cikin matakan da kundin tsarin mulkin ya tanada kafin kirkirar sabuwar jiha.

Ya ce:

“Amma a ganina, a yanzu ya kamata mu dakatar da batun, mu bar jihohin da ake da su su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.”

Sakon gwamna Dauda ga masu mukamai

An ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya ce jami’in da yake ganin bai amfana da gwamnatinsa ya kamata ya yi murabus daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan more rayuwa sama da N20bn a kowace ƙaramar hukuma cikin shekaru uku.

Gwamnan ya yi kira ga ’yan APC da su daina rarrabuwa zuwa gidajen siyasa tare da haɗa kai a ƙarƙashin jam’iyya guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.