Dan Takarar PDP, Wasu 3000 Sun Yi Watsi da Jam’iyyunsu, Sun Koma APC
- Ɗan takarar PDP, Hammed Taoreed Ademola, da ɗan takarar Accord, Adedapo Ojo, sun koma APC tare da magoya bayansu
- Ademola ya ce bincikensa ya tabbatar masa cewa tikitin wata jam’iyya banda APC ba zai kai ɗan takara ko’ina a zaɓen 2027 ba
- Shugaban APC na Oyo, Moses Alake-Adeyemo, ya yi maraba da sababbin mambobin, yana mai ba su tabbacin samun dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Jam'iyyar PDP ta sake yin bari bayan rashin jiga-jiganta da wasu dubban mambobi da suke yi watsi da ita.
Ɗan takarar PDP na mazabar Ibadan ta Arewa maso Gabas a zaɓen 2027, Hammed Taoreed Ademola, da ɗan takarar Accord, Adedapo Ojo, sun koma jam'iyyar APC.

Source: Twitter
Ademola, wanda aka fi sani da Lucky, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP ne bayan ya gudanar da bincike kan yanayin siyasar ƙasar, cewar Tribune.
Binciken da ya jawo Ademola ya koma APC
Ya ce bincikensa ya nuna cewa duk wani tikitin jam’iyya banda APC tamkar takarda ce kawai, wadda ba za ta kai ɗan takara ko’ina ba.
Ademola ya ce shi da ɗaruruwan magoya bayansa sun shiga APC a hukumance, tare da yin alkawarin aiki domin ci gaban jam’iyyar da Najeriya.
Ya ce:
“Na gudanar da bincike mai zurfi, kuma na fahimci cewa duk wani tikiti da ba na APC ba, takarda ce kawai wadda ba za ta kai ɗan takara ko’ina ba a zaɓen 2027. Mun zo nan ɗaruruwanmu ne domin shiga APC a hukumance, kuma mun yi alkawarin yin iya ƙoƙarinmu domin amfanin jam’iyya mai kishin ci gaba da kuma ƙasarmu ƙaunatacciya, Najeriya.”
Ojo ya bayyana Accord a matsayin wata hanya da ke ɗauke hankalin jama’a, inda ya ƙarfafa masu zaɓe su ci gaba da mara wa APC baya.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Source: Original
Alkawarin APC ga sabbabin yan jam'iyyar
Da yake karɓar sababbin mambobin, shugaban APC na Oyo, Moses Alake-Adeyemo, ya tabbatar musu cewa za su samu dama daidai da sauran ’yan jam’iyya.
Alake-Adeyemo ya bukaci sababbin mambobin su yi aiki tuƙuru domin ganin dukkan ’yan takarar APC sun samu nasara a babban zaɓen 2027, cewar Punch.
Ya ce zaɓen mai zuwa wata dama ce ta sake rubuta tarihin Najeriya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan baƙaƙen fata a duniya duba da yawan arzikin da Ubangiji ya yi mata.
Jigon APC ta bar APC a Zamfara
An ji cewa jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Hajiya Hadiza Liman, ta fice daga jam’iyyar tare da magoya bayanta zuwa jam'iyyar NDC.
Hadiza ta ce ta koma NDC ne saboda zargin cewa Gwamna Dauda Lawal ya yi watsi da ita da magoya bayanta duk da irin goyon bayan da suka ba shi.
Ta ce za ta mara wa ɗan takarar gwamnan NDC, Sanata Kabiru Garba Marafa, baya tare da magoya bayanta a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
