Duniya Labari: Hotunan Yadda Aka Gudanar da Jana’izar Bamanga Tukur a Adamawa
- An birne tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Bamanga Tukur, a garinsu Yola da ke Adamawa, bayan rasuwarsa yana da shekaru 91
- An gudanar da jana’izar Tukur bisa tsarin addinin Musulunci, inda aka birne gawarsa a gidan iyalansa da ke Fadde-Sanda kan hanyar Abuja
- Shugaba Tinubu ya bayyana Tukur a matsayin fitaccen mutum a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya, yayin da manyan jami’ai suka halarci jana’izar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - An birne gawar tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, Bamanga Tukur, a garinsu Yola da ke Adamawa ranar Lahadi.
Tsohon shugaban PDP, Bamanga Tukur ya rasu bayan fama da jinya a ranar Asabar 12 ga watan Satumbar 2026 da muke ciki yana da shekaru 91 a duniya.

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ne bisa tsarin addinin Musulunci, karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Modibbo Adama da ke Yola, Ahmadu Bobboi.
Tinubu ya yi jimamin mutuwar Bamanga Tukur
A ranar Asabar 12 ga watan Satumbar 2026, Shugaba Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar Tukur, inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen mutum a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.
Tukur ya taɓa zama gwamnan tsohuwar jihar Gongola, sannan ya kasance Ministan Masana’antu a Najeriya inda ya ba da gudunmawa mai yawa.
Hakan na cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar wanda Legit Hausa ta bibiya.
A cikin sanarwar, Tinubu ya bayyana Tukur a matsayin “fitaccen mutum ƙwarai” wanda aikinsa ya shafi gudanar da harkokin gwamnati, shugabanci, masana’antu, siyasa da harkokin kasuwanci a Afirka.

Source: Facebook
Yadda aka yi jana'izar Bamanga Tukur a Adamawa
Tukur ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 18, ciki har da Sakataren Gwamnatin Adamawa, Awwal Tukur, cewar Vanguard.
An birne gawar Tukur a gidan iyalansa da ke Fadde-Sanda a kan hanyar Abuja, Yola da ke jihar Adamawa da misalin ƙarfe 11:30 na safe.
Manyan mutane da dama sun halarci sallar jana’izarsa, ciki har da Aliko Dangote, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, Sanata Iya Abbas mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya da tsohon Gwamna Jibrilla Bindow.
Haka kuma, sarakunan gargajiya da sauran manyan baki daga Adamawa da wajen jihar sun halarci jana’izar.
Al'umma da dama da suka halarci jana'izar sun bayyana dattijon a matsayin mutumin kirki inda suka yi masa addu'ar Ubangiji ya gafarta masa ya ba shi gidan aljanna.

Source: Facebook

Source: Facebook

Source: Facebook
Bamanga: An ayyana makokin kwana 3 a Adamawa
Mun ji cewa Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana zaman makoki nankwanaki uku kan rasuwar Alhaji Bamanga Tukur.
Fintiri ya umarci a sauke tutar jihar zuwa rabin sanda na tsawon kwanaki uku domin karrama marigayin wanda ya ba Najeriya gudunmawa mai yawa.
Tukur, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya rasu da sanyin safiyar Asabar 12 ga watan Satumbar 2026 bayan gajeriyar rashin lafiya .
Asali: Legit.ng

