‘Sharri Ne’: Malami Ya Ce Bai Yi wa Tinubu, Shettima Addu’a Su Yi Nasara ba

‘Sharri Ne’: Malami Ya Ce Bai Yi wa Tinubu, Shettima Addu’a Su Yi Nasara ba

  • Rabaran Ezekiel Dachomo ya ya martani kan yada cewa ya yi wa Bola Tinubu da Kashim Shettima addu’ar samun nasara
  • Limamin ya ce ziyararsa Isra’ila na da nufin jawo hankalin duniya kan matsalolin tsaro da abin da ya kira tsananta wa Kiristoci
  • Dachomo ya bayyana cewa addu’arsa ita ce Najeriya ta samu nasara tare da zaman lafiya ga Musulmi da Kiristoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Shugaban Cocin Christ in Nations (COCIN), Rev. Ezekiel Dachomo, ya karyata jita-jitar da ake yadawa kansa bayan ya je Isra'ila.

Dachomo ya musanta rahotannin cewa ya yi wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima addu’ar samun nasara a zaben 2027.

Fasto ya musanta yi wa Tinubu da Shettima addu'a
Fasto Ezekiel Dachomo da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Rev. Ezekiel Dachomo, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Malamin ya yi wannan bayani ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Litinin 5 ga watan Oktobar 2026.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu

Dachomo, wanda a halin yanzu yake Isra’ila domin wani rangadin wayar da kan duniya kan Kiristanci, ya ce manufarsa ita ce jawo hankalin shugabannin duniya kan halin da Kiristocin Plateau ke ciki.

Dachomo ya yi karin haske kan addu'a a Isra'ila

Faston ya ce an yi wa wani sakonsa na baya, inda ya yi wa Najeriya addu’a, mummunar fahimta har aka dauke shi a matsayin goyon bayan Tinubu da Shettima gabanin zaben 2027.

Ya ce babu inda a cikin sakon nasa ya yi addu’ar Shugaban kasa da Mataimakinsa su yi nasara a zaben.

Dachomo ya ce addu’o’insa sun mayar da hankali ne kan jin dadin Najeriya da nasarar al’ummar kasar, ba tare da la’akari da addininsu ba.

Ya ce:

“Mutane suna kokarin nuna kamar na yi wa tikitin Musulmi da Musulmi addu’a. Amma ban yi ba, kuma ba zan taba yin addu’ar tikitin Musulmi da Musulmi ba, domin Najeriya ta kowa ce, Musulmi da Kirista.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da abokinsa suka kusa fada wa gadar Legas a hadarin mota

“Ina yi wa Musulmi da Kiristoci a Najeriya addu’a. Ina yi wa Najeriya addu’ar samun nasara. Idan da gaske kake son kusantar Allah, ka zo da zuciya mai tsabta.”
Fasto Dachomo ya musanta yi wa Tinubu addu'a
Fasto Ezekiel Dachomo da ke yawan korafi kan kisan Kiristoci. Hoto: Rev. Ezekiel Dachomo.
Source: Facebook

Zargin da Dachomo ke yi a Plateau

Malamin ya ce bai yi wa Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaba Shettima addu’ar samun nasara a 2027 ba kuma ba zai taba yi masu ba.

Wannan bayani na Dachomo ya zo ne yayin da ake mayar da martani kan rangadin da yake yi a Isra’ila, inda yake neman jawo hankalin duniya kan matsalolin tsaro da kuma abin da ya bayyana a matsayin tsananta wa Kiristoci a Plateau.

Yadda aka sauke shafin Facebook na Dachoma

A baya, mun kawo muku cewa mutane da dama sun yi korafi bayan tabbatar da cewa an goge shafin Facebook na Fasto da yake ikirarin kisan Kiristoci wanda ya tayar da kura.

Fasto Ezekiel Dachomo da kansa ya tabbatar da haka ga wasu manema labarai lamarin da ya fara jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin masoyansa.

Dachomo ya shahara da ya bayyana cewa ya gudanar da jana’izar gawarwaki sama da 67, tare da gabatar da shaida a gaban Majalisar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.