An Gindaya wa Nyesom Wike Sharuɗa 2 game da APC kafin Zaben 2027

An Gindaya wa Nyesom Wike Sharuɗa 2 game da APC kafin Zaben 2027

  • Tsohon kakakin Shugaba Tinubu a Kudu maso Gabas, Denge Josef Onoh, ya ba Nyesom Wike sharadi
  • Onoh ya ce kungiyar “Rainbow Coalition” da Wike ke jagoranta na iya raba kan APC tare da rage mata damar samun nasara a zaben 2027
  • Ya kuma zargi Wike da kai hare-hare kan wasu gwamnonin APC, yana mai cewa hakan na iya raunana tsarin jam’iyyar da kuri’un APC a jihohi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon kakakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kudu maso Gabas, Denge Josef Onoh, ya ba Nyesom Wike shawara kan zaben 2027.

Onoh ta bukaci Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya shiga APC ko ya janye daga harkokin jam’iyyar.

An gargadi Wike kan shiga lamarin APC
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Nyesom Wike. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Jigon APC ya gargadi Wike kan lamarin APC

Onoh ya bayyana kawancen siyasar da Wike ke tallatawa da sunan “Rainbow Coalition”, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Kashe kashe ya yi yawa': An taso gwamna a gaba sai ya bar kujerarsa

Ya yi gargadin cewa kawancen na iya raunana jam’iyyar APC mai mulki gabanin babban zaben 2027, musamman idan aka bar shi ya haifar da rarrabuwar kawuna.

Ya ce:

“Wannan abin da ake kira ‘Rainbow Coalition’ wata karkatarwa ce mai guba, mafarki ne na siyasa, kuma wata hanya ce da aka tsara domin cimma muradin kai, wadda a karshe za ta raunana APC tare da jefa zaben shugaban kasa cikin hadari idan ba a dakile ta ba.”

A cewar Onoh, kawancen bai wakilci dunkulalliyar kungiyar siyasa da za ta iya samar wa Shugaba Tinubu gagarumin adadin kuri’u daga wajen Jihar Rivers ba.

Ya ce tasirin siyasar Wike ya fi karkata ne zuwa Jihar Rivers, inda ya nuna shakku kan yunkurin yada abin da ya kira “tsarin da ya rabu” zuwa sauran yankunan siyasar kasar.

‘Rainbow Coalition ba G5 na 2023 ba’

Onoh ya kuma yi watsi da kwatanta kawancen siyasar da ake yi yanzu da kawancen gwamnonin G5 da ya kunno kai gabanin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai ragargaji Atiku da Tinubu a zaben 2027 a Kano

Ya ce G5 an gina shi ne bisa adalcin rabon mukamai da yankuna, kuma ya kunshi gwamnonin jihohi biyar masu rike da madafun iko kan tsarin siyasar jihohinsu.

Onoh ya tuna da rawar da ya taka wajen kokarin bunkasa APC a Kudu maso Gabas lokacin da yake aiki tare da tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi.

Ya ce sauye-sauyen siyasar da suka faru a wancan lokaci sun janyo asara ga wasu daga cikin ’yan siyasar da abin ya shafa, cewar Vanguard.

‘Wike dole ya bayyana matsayarsa'

Onoh ya bukaci Wike ya bayyana matsayinsa na siyasa karara, yana mai cewa ministan ba zai iya ci gaba da abin da ya kira biyayya ga bangarori biyu ba tare da kokarin yin tasiri kan harkokin APC ba.

Ya ce:

“Babu gurbi a siyasar Najeriya ga masu wasa da bangarori biyu, masu karbar kudin haya na siyasa ko masu biyayya na dan lokaci.
“Ba za ka iya sanya kafa daya a PDP, dayan kuma ta kasance tana shawagi a wani kawance mara tabbas, sannan ka yi tsammanin za ka rika tsara makomar APC da tsarin cikin gida.”

Kara karanta wannan

2027: Pantami ka iya goyon bayan Tinubu a kaikaice saboda tasirin Wike a sama

Onoh ya ce APC tana da tsarin jam’iyya da goyon bayan jama’a a matakin kasa da zai ba ta damar taimaka wa Tinubu samun nasara a jihohi 36, ba tare da abin da ya kira “karkatarwar Wike mai cutarwa da son kai” ba.

Dan takarar shugaban kasa zai ba Wike 'mukami'

A wani labarin, an ji cewa dan takarar SDP, Adewole Adebayo, ya ce zai iya nada Nyesom Wike minista idan ya zama shugaban Najeriya, amma zai takaita kalaman jama’a na ministan.

Adebayo ya yaba da kwazon Wike wajen ayyukan raya Abuja, yana cewa ayyukan more rayuwa da yake jagoranta sun saukaka zirga-zirga.

Duk da yaba masa, Adebayo ya soki salon siyasar Wike da yadda yake bayyana ra’ayoyinsa, yana cewa zai “liƙa tef a bakinsa” idan ya nada shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.