Yadda Lauyoyi Suka Fafata a Shari'ar Sheikh Lawal Triumph a Kotun Kano

Yadda Lauyoyi Suka Fafata a Shari'ar Sheikh Lawal Triumph a Kotun Kano

  • Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a Kano ta yi fatali da ƙalubalantar huruminta na sauraron ƙarar da aka shigar kan Malam Lawan Abubakar Triumph
  • Lauyan masu ƙara ya buƙaci kotun ta umarci ’yan sanda su gudanar da bincike kan zargin ɓatanci ga addini da ake yi wa malamin
  • Lauyan Malam Lawan ya ƙalubalanci hurumin kotun, sai dai Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da ci gaba da sauraron ƙarar tare da neman ƙarin wasu bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a ƙwaryar birnin Kano ta yi fatali da ƙalubalen huruminta na sauraron ƙarar da wasu ƙungiyoyin Musulunci suka shigar kan Malam Lawan Abubakar Triumph.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya jagoranci zaman kotun a ranar Litinin, inda ya yi fatali da hujjojin da lauyan malamin ya gabatar na neman kotun ta yi watsi da ƙarar.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta shirya yanke hukunci a bukatar da El Rufai ya dade yana nema

Lawan Abubakar Triumph.
Sheikh Lawan Abubakar Triumph yana darasi. Hoto: Sheikh Lawan Abubakar Triumph.
Source: Facebook

Aminiya ta rahoto cewa ƙungiyoyin sun shigar da ƙarar ne kan zargin ɓatanci ga addini da ake yi wa Malam Lawan Triumph, tare da neman a gudanar da bincike kan lamarin.

An ƙalubalanci hurumin kotun

Tun da farko, lauyan Malam Triumph. Barista Abdurrazak Ahmad, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa ba ta da hurumin sauraron ta.

Ya ce ƙungiyoyin da suka shigar da ƙarar sun taɓa gabatar da makamanciyar ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano.

Lauyan ya kuma yi zargin cewa ƙungiyoyin ba su da ikon shigar da ƙarar saboda ba su gabatar da shaidar rajistarsu ba.

A cewarsa, doka ta bai wa ƙungiyoyin da aka yi wa rajista damar shigar da irin wannan ƙara, yayin da ya ce Babbar Kotun Tarayya ce ke da hurumin sauraron batun, ba Kotun Shari’a ba.

Lauyan masu ƙara ya yi martani

Sai dai lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Haji, ya musanta hujjojin da ɓangaren kariya ya gabatar, inda ya ce Kotunan Shari’a suna da hurumin sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Yadda fusatattun matasa suka so lakada wa Rarara duka kan tallata Tinubu

Barista Haji ya buƙaci kotun ta umarci ’yan sanda su gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa malamin domin tabbatar da adalci.

Ya kuma gabatar wa kotun da takardun rajistar ƙungiyoyin, yana mai cewa ba a gabatar da su a baya ba ne saboda ba a buƙace su ba.

Kotun za ta ci gaba da shari’ar

Lauyan wanda ake ƙara ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa ƙungiyoyin da aka gabatar da takardun rajistarsu ba su ne waɗanda aka ambata a matsayin masu ƙara a shari’ar ba.

Dangane da hakan ne lauyan ya buƙaci kotun ta yi la’akari da takardun kafin ta yanke matsaya.

A nasa ɓangaren, Barista Haji ya zargi ɓangaren malamin da ƙoƙarin amfani da ƙananan batutuwan fasaha wajen kawo cikas ga shari’ar.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya ce mutum na iya shigar da ƙara ba tare da an sanya sunan ƙungiya a cikinta ba, yana mai cewa za a iya gudanar da binciken ’yan sanda daga baya da sunan ƙungiyoyin ko gwamnatin Jihar Kano.

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yi fatali da ƙalubalantar hurumin kotun, inda ya amince da ci gaba da sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun yi masa raddi mai zafi

Kotun ta kuma umarci masu ƙarar su gabatar da kwafin takardun rajistar ƙungiyoyin domin a duba su kafin sanar da ranar ci gaba da sauraron ƙarar.

Nafiu Baba-Ahmed ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sakatare-Janar na Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed, ya rasu a safiyar Talata, 6 ga Oktoba, 2026.

Marigayin ya kasance malamin addinin Musulunci, lauya kuma mai fafutukar tabbatar da adalci, yayin da manyan malaman Musulunci suka bayyana shi a matsayin mutum mai haɗa kan jama’a.

Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da Sallar Jana’izarsa a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja bayan Sallar Azahar a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng