Tofa: Tsagin ADC Ya Dakatar da Atiku Abubakar da Babachir Lawal daga Jam'iyyar

Tofa: Tsagin ADC Ya Dakatar da Atiku Abubakar da Babachir Lawal daga Jam'iyyar

  • Wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ƙarƙashin Raji Zumo ya yi taron sanar da dakatar da Atiku Abubakar da wasu mutane biyu daga jam'iyyar
  • Raji Zumo ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassan bogi a jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da yin watsi da umarnin kotu
  • Sai dai Babachir Lawal, wanda shi ma aka dakatar da shi, ya bayyana kwamitin Raji a matsayin "masu shan wiwi" wadanda ƙwaya ta bugar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Adamawa – Wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ya sanar da dakatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bisa zargin sa da janyo rarrabuwar kai a cikin jam'iyyar.

Shugaban tsagin na ADC a Adamawa, Raji Zumo, ne ya sanar da wannan mataki yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026, a garin Yola.

Kara karanta wannan

An zabi sabon shugaban ADC a Kano bayan shigar Kwankwaso, mutane 27 sun samu mukami

Jam'iyyar ADC ta dakatar da Atiku Abubakar, Babachir Lawal
Babachir Lawal (hagu), tambarin jam'iyyar ADC (tsakiya) da Atiku Abubakar (dama). Hoto: @ADCngcoalition, @atiku
Source: Twitter

Tsagin ADC ya dakatar da Atiku, Babachir Lawal

Baya ga Atiku, jam'iyyar ta kuma dakatar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da kuma shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar, Sadiq Ibrahim, in ji rahoton The Cable.

A cewar Raji Zumo, dakatarwar ta zama dole domin kare martabar jam'iyyar da kuma tabbatar da bin doka da oda.

Ya bayyana cewa:

"Babu wani mutum, ko yaya girmansa ko tasirinsa, da ya fi ƙarfin doka ko kundin tsarin mulkin ADC matuƙar shi halastaccen mamba ne na jam'iyyar."

Raji Zumo ya ƙara da cewa an ɗauki wannan matakin ne bayan tuntubar jami'an zartarwa na jam'iyyar, inda ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassa na bogi a cikin jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da kuma yin watsi da umarnin kotu.

Rikicin shugabancin ADC a matakin kasa

Wannan takun-saƙa na faruwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ADC ke fuskantar babban rikicin shugabanci tun daga watan Yulin 2025, lokacin da wata ƙungiyar haɗin gwiwa ta ƴan hamayya ta karɓi ragamar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan tattaunawar Iran da Amurka ta rushe, an harba wasu makamai kan Isra'ila

Ana fafatawa tsakanin Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, da kuma David Mark, wanda ake zargin an naɗa shi ba bisa ƙa'ida ba.

A ranar 1 ga Afrilu, 2026, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke amincewa da tsagin David Mark biyo bayan hukuncin wucin gadi na Kotun ɗaukaka ƙara.

Ana sa ran Kotun Ƙoli za ta saurari ƙarar da David Mark ya shigar a gobe Talata, 14 ga Afrilu, 2026, domin yanke hukunci kan wanda yake shugabancin jam'iyyar ADC na gaskiya.

Babachir Lawal ya ce duk wadanda suka kore su daga ADC 'yan wiwi ne.
Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: Babachir David Lawal
Source: Facebook

"Yan wiwi ne," - Martanin Babachir Lawal

Babachir Lawal, ya mayar da zafafan martani kan iƙirarin dakatar da shi da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam'iyyar.

Da yake magana da jaridar Punch, Babachir Lawal, wanda shi ne Mataimakin Shugaban jam'iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Gabas, ya bayyana masu sanar da dakatarwar a matsayin mutanen da ƙwaya ta bugar.

"Idan wasu mutane suka sha wiwi sosai, za su iya iƙirarin cewa su ne Shugaban Ƙasar Najeriya, don haka kada ku ɗauke su a matsayin mutane na gari. Tasirin wiwi ne ke aiki," in ji Babachir.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan takarar gwamna ya ragewa NNPP ƙarfi a Katsina gabanin 2027

Ya ƙara da cewa Raji Zumo ba shi da wani muƙami a cikin ADC da zai ba shi damar yin magana a madadin jam'iyyar.

Atiku ya samu goyon baya a ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da ADC ke cigaba da yi wa mutane rajista, daya daga cikin manyan jam'iyyar, Dele Momodu ya nuna goyon baya ga Atiku Abubakar.

Cif Momodu ya bayyana haka ne yayin wata hira da 'yan jarida, inda ya ce ya kamata jam'iyyar ADC ta ba 'yan Arewa damar yin takara.

Hakan na zuwa ne yayin da manyan 'yan siyasa kamar Peter Obi, Rotimi Ameachi da sauransu ke nuna sha'awar yin takara a ADC a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com