Sheikh Pantami Ya Ji Ƙamshin Nasara da Ya Samu Gagarumin Goyon Baya gabanin Zaben 2027
- Tsohon kwamishinan Gombe, Muhammad Ismail City ya fice daga APC tare da bayyana goyon bayansa ga Isa Ali Pantami a zaɓen gwamna na 2027
- Tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Akko ya ce Gombe na buƙatar shugaba mai mutunci da ƙwarewar zamani ta duniya
- Muhammad ya bayyana Pantami a matsayin jagora mai hangen nesa da ƙwarewar sauya tsarin mulki da ci gaban tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Tsohon kwamishina a Jihar Gombe kuma tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Akko, Hon. Muhammad Ismail City (Katukan Akko), ya fice daga Jam’iyyar APC.
Jigon siyasar na jihar Gombe ya kuma bayyana goyon bayansa ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, gabanin zaɓen gwamna na 2027.

Source: Facebook
Farfesa Suleiman Mohammed Gombe na Pantamiyya Movement ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a shafin Pantami na Facebook.
Muhammad, wanda ya taɓa zama kwamishina mai zaman kansa a Hukumar Zaɓe ta Gombe (GOSIEC), ya sanar da matakin nasa ne yayin wata ganawa da Pantami a ofishin tsohon ministan.
Dalilin sauya shekar tsohon kwamishina
Mohammed ya ce ƙwarewarsa a harkokin zaɓe da shugabancin ƙaramar hukuma ta ba shi damar fahimtar irin halayen da ake buƙata wajen samar da shugabanci nagari a jihar.
Ya ce Gombe na kan wani muhimmin mataki da ke buƙatar shugaba mai mutunci, gogewa a harkokin duniya da kuma tarihin ingantaccen shugabanci mai kawo sauyi.
Ya bayyana Pantami a matsayin jagora mai hangen nesa, yana mai kawo misalin lokacin da ya yi a matsayin shugaban hukumar NITDA, sannan daga baya ya zama Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani.
A cewarsa, Pantami ya nuna a lokacin da yake hidimar jama’a cewa yana da ƙwarewar jagorantar kirkire-kirkire, sauye-sauyen da kuma tsara dabarun ci gaba.

Source: Twitter
Dalilin goyon bayan Sheikh Pantami

Kara karanta wannan
An fara fito da abubuwan da Tinubu ya shirya yi a Najeriya idan ya lashe zaben 2027
Ya kuma bayyana tsohon ministan a matsayin masani da ya yi ƙaurin suna a duniya wanda ke da ƙwarin gwiwa wajen bunƙasa ɗan Adam, ƙarfafa matasa da kuma inganta ababen more rayuwa.
“Bayan na yi nazari sosai kan yanayin siyasar ƙasar da kuma buƙatun al’ummarmu, na gamsu ƙwarai cewa Farfesa Pantami yana da ƙwarewar gudanarwa ta musamman da ake buƙata domin ɗaga Jihar Gombe zuwa matakin da ba ta taɓa kaiwa ba,” in ji shi.
Saboda haka, ya yi kira ga abokan siyasarsa, masu ruwa da tsaki a Ƙaramar Hukumar Akko da sauran ’yan Jihar Gombe da su goyi bayan burin Pantami na zama gwamna a Gombe.
Pantami na da kwarin gwiwar nasara
Kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben gwamna a 2027.
Malamin ya nanata cewa mutane ne suka nemi ya shiga siyasa kuma ya amsa kira bayan ya yi addu'o'i da istikara duk da bai so hakan ba a farko.
Asali: Legit.ng
