‘Babban Abin da Zai Raba Bola Tinubu da Mulkin Najeriya a 2027’

‘Babban Abin da Zai Raba Bola Tinubu da Mulkin Najeriya a 2027’

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ce matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa sun yi tasiri a mulkin Bola Tinubu wajen tantance
  • Sakataren yada labaran ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi watsi da hasashen cewa Tinubu na iya lashe zaben 2027
  • Abdullahi ya ce APC ba za ta iya samun nasara ta hanyar magudin zabe ba, yana mai cewa jam’iyyarsu na da dabarun dakile hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana matsaar da za ta kawo karshen Bola Tinubu a Najeriya.

ADC ta ce matsalar tsadar rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta za ta fi addini ko kabila tasiri a zaben shugaban kasa na 2027.

ADC ta dura kan gwamnatin Bola Tinubu
Kakakin ADC a Najeriya, Bolaji Abdullahi da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Malam Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana haka yayin hira da Arise News a Abuja.

Kara karanta wannan

Amaechi ya fayyace saukin da za a samu tun shekarar farko idan Atiku ya kafa gwamnati

ADC ta yi watsi da hasashen nasarar Tinubu

Abdullahi ya yi watsi da wani rahoto da ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu na iya lashe zaben 2027 duk da rashin farin jininsa.

Ya ce rahoton ya fi mayar da hankali kan rawar da addini da kabila za su iya takawa a zaben, amma ya ce an yi karin gishiri kan wannan batu.

Abdullahi ya ce:

“Muna ganin labarin ya ginu ne kan wasu zato wadanda ba lallai ne su kasance daidai ba. Mun amince da cewa Shugaba Tinubu ba shi da farin jini a ko’ina, amma mun yi sabani da cewa zai iya lashe zaben.
"Yan Najeriya daga kowane bangare sun hadu ne karkashin matsalar tsadar rayuwa da gwamnatin Tinubu ta jefa su ciki.”
Tinubu ya sha suka daga ADC
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da ke ba ADC mamaki game da Tinubu

Rahoton ya kuma nuna cewa Shugaba Tinubu bai bayyana kamar yana cikin damuwa kan yiwuwar rashin nasara a zaben ba.

Kara karanta wannan

Amaechi ya zargi Shugaban kasa Tinubu da hannu a mutuwar mahafiyarsa

Abdullahi ya ce idan hakan gaskiya ne, to shugaban bai fahimci yanayin da ake ciki a kasar ba.

“Kuma wannan ne zai fi komai tasiri wajen tantance yadda za su kada kuri’arsu.
“Hanya daya tilo da APC za ta iya tunanin samun nasara a zaben ita ce ta hanyar magudin zabe. Mun san hakan, kuma muna da dabarun dakile su.”

Martanin jam'iyyar ADC na zuwa ne yayin da ake ta shirye-sheiyen gudanar da zaben shekarar 2027 wanda ake hasashen zai yi matukar zafi fiye da sauran zabubbua da aka yi a baya.

Tinubu Must Go: ADC ta fusata kan cafke matasa

An ji cewa reshen jam’iyyar ADC na Borno ya yi Allah-wadai da kama wasu matasa biyar da aka ce jami’an tsaro sun cafke saboda sanya rigunan “Tinubu Must Go”.

ADC ta ce kama matasan ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin faɗin ra’ayinsu inda ta bukaci sakinsu da gaggawa.

Jam’iyyar ta bukaci a saki matasan ba tare da wani sharadi ba, tare da neman afuwa daga jami’an tsaro da kare ’yancin dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.