Pantami Ya Ce ba Ya Fargabar Cin Zaben 2027, Ya Fadi Irin Mulkin da zai Yi a Gombe

Pantami Ya Ce ba Ya Fargabar Cin Zaben 2027, Ya Fadi Irin Mulkin da zai Yi a Gombe

  • Dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben gwamna a 2027
  • A wata hira da ya yi, Pantami ya bayyana cewa babu alamar jin tsoro ko dardar a takarar da ya ke yi kuma zai fuskanci dukkan kalubalen jihar
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin fara kamfen din gwamna na 2027 a Najeriya, inda siyasar jihar Gombe ke daukar hankali sosai a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Sheikh Isa Ali Pantami ya jaddada cewa yana nan a kan bakar shi ta shiga siyasa da neman takarar gwamna a zaben 2027.

Malamin ya nanata cewa mutane ne suka nemi ya shiga siyasa kuma ya amsa kira bayan ya yi addu'o'i da istikara duk da bai so hakan ba a farko.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta shiga Aso Rock ta dauke ma’aikacin da ya yi aiki da shugabannin kasa 3

Sheikh Pantami a wajen wa'azi
A lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami ya ke wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Shekh Isa Ali Pantami ya bayyana haka ne a wata hira da tasahar DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kalubalen jihar Gombe

Pantami ya bayyana cewa jihar Gombe na fama da matsaloli da dama duk da cewa kowa yana zuwa ya yi iya kokarinsa ya tafi.

Ya bayyana cewa Muhammadu Danjuma Goje da Ibrahim Hassan Dankwambo sun yi kokari wajen samar da makarantu da manyan cibiyoyi a jihar.

Haka zalika ya ce Inuwa Yahaya ya samar da gandun masana'antu da shi a yanzu yana da tsarin kawo yadda wajen zai amfani jihar.

Saboda haka Pantami ya ce zai mayar da hankali ne wajen samar da cigaban dan Adam domin gina mutum ya samu cigaba sosai.

Pantami ya ce talauci ya yi yawa a Gombe kuma ana fama da yawan yaran da ba su zuwa makaranta a jihar.

Game da gina dan Adam, Pantami ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

"Da na ce zan kashe biliyoyi na gina gidan gwamnati, gwara na kashe kudin wajen gina dan Adam, ya fi muhimmanci."

Maganar daukar mutane aiki

Pantami ya ce zai mayar da hankali wajen kulla hulda da kasashen waje domin su shigo jihar Gombe su gina kamfanoni su samawa mutane aiki..

Ya ce yana da tsare-tsare da zai kawo wajen ba matasa horo su samar wa kansu sana'o'i da kuma inganta sana'ar da suke yi.

Pantami ya kuma bayyana cewa zai mayar da hankali kan mata, 'yan kasuwa da wadanda ba su zuwa makaranta da sauransu.

Karbuwar Pantami a Gombe

Pantami ya bayyana cewa yana da tsarin siyasa da ya kun shi sama da mutum 20,000 da za su yi masa aiki kuma yana karbuwa a jihar.

Dan takarar ya bayyana cewa masu ba shi goyon baya a jihar Gombe sun fi mutanen da suke nuna goyo baya a kafafen sada zumunta yawa.

Sheikh Pantami a jihar Gombe
Lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Malam ya ce ba ya fargaba a kan cewa zai yi nasara a zaben jihar Gombe na 2027, inda ya ce masu fargabar sun san kansu.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya bayyana gwamna 1 da ya cancanci zama shugaban ƙasar Najeriya

Pantami ya bayyana cewa 'yan dangwale da dama sun tarbe shi a wurare da dama da ya shiga kananan hukumomin jihar Gombe kwanakin baya.

Goje ya ce yana APC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje, ya yi watsi da jita-jitan da ake yi cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC.

Goje ya yi karin bayanin ne bayan daruruwan magoya bayansa daga Gombe ta Tsakiya da makwabtansu sun ziyarci gidansa.

Mataimakinsa na musamman kan kafofin labarai, Ahmed Kashere, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng