Gwamna Ya Nemi Alfarmar Musulmi game da Zaɓen Tinubu, Ya Yi Masu Alƙawari
- Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya roƙi Musulman jihar su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Oyebanji ya ce gwamnatin Tinubu ta taimaka wajen ci gaban Ekiti, yana mai alkawarin ci gaba da ba Musulmi dama a gwamnatinsa
- Shugaban Ƙungiyar Limamai da Alfas ta Kudu maso Yamma, Jamiu Kewulere Bello, ya yabawa Oyebanji kan tsarin mulki mai bai wa kowa dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ekiti - Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya nemi alfarma ga al'ummar jihar domin sake ba Shugaba Bola Tinubu dama a zaɓen 2027.
Gwamna Oyebanji ya roƙi Musulman jihar da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Oyebanji ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a yayin wata addu’ar godiya ta musamman a Babban Masallacin Ado-Ekiti, cikin shirye-shiryen fara wa’adinsa na biyu, cewar The Nation.
Gwamna ya roƙi al'ummar Musulmi kan Tinubu
Gwamnan ya ce Musulmi su goyi bayan Tinubu domin nuna godiya ga matakan tallafi da gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen bunƙasa Ekiti.
Oyebanji ya kuma tabbatar wa al’ummar Musulmi cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsarin mulki mai bai wa kowa dama, ba tare da nuna bambanci ba.
Ya gode wa al’ummar Musulmi saboda addu’o’insu da goyon bayan da suka ba gwamnatinsa a wa’adin farko, yana mai cewa addu’o’insu sun taimaka wajen samun nasarori.
Gwamnan ya roƙi Musulman jihar da su ci gaba da yi wa gwamnatinsa addu’a yayin da yake fara wa’adinsa na biyu.
Ya ce:
“Na zo ne domin gode wa Allah da mahaifina, Babban Limami. Ina godiya da goyon bayan da kuka ba mu. Ina kuma godiya ga al’ummar Musulmi saboda addu’o’inku.
“Ina roƙonku a yau da ku ci gaba da yi mana addu’a domin mu samu damar yin abubuwa da dama. Ina tabbatar muku cewa gwamnatina za ta tabbatar an ƙara ba Musulmi dama su yi hidima a wa’adinmu na biyu.”
Ya ce Musulman da aka naɗa cikin gwamnatinsa ta farko sun yi rawar gani sosai, yana mai cewa ya tuntubi Babban Limamin kafin zaɓar su, cewar Punch.

Source: Twitter
Alkawarin da Gwamna Oyebanji ya yi
Oyebanji ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta zaman lafiya, haɗin kai da haƙurin addinai, tare da tabbatar da cewa kowa yana da matsayi a gwamnati.
“Dole in faɗi hakan a bainar jama’a, duk Musulman da suka yi aiki tare da ni sun yi rawar gani sosai. Hikimar da na yi amfani da ita lokacin naɗinsu ita ce tuntubar Babban Limami, wanda ya zaɓo min mafiya dacewa, kuma ina gode musu saboda kyakkyawan aikin da suka yi."
in ji shi.
Ya kuma yi kira da a ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, cibiyoyin addini da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
An gargadi Atiku kan kiran Tinubu da Bola
Mun ba ku labarin cewa tsohon darektan yakin neman zaben Peter Obi, Akin Osuntokun, ya soki Atiku Abubakar kan yadda yake kiran Shugaba Tinubu.
Osuntokun ya ce Atiku na da damar sukar Tinubu da gwamnatinsa, amma kiransa da sunansa ya saba wa mutuncin ofishin.
Ya ce masu adawa da Tinubu suna da hanyoyin kundin tsarin mulki na neman sauya gwamnati, ciki har da zabe ko tsige shugaban kasa
Asali: Legit.ng


