Jami’an Tsaro Sun Yi Barazanar Cafke Sanusi II da Aminu Ado Bayero a Kano
- Jami’an tsaro a Kano sun yi barazanar kama Sarakunan Kano na 16 da 15, Sanusi II da Aminu Ado Bayero
- Hedikwatar tsaron ta ce har yanzu dokar hana hawan doki da gudanar da durbar tana nan, kuma ta shafi kowa
- Matakin ya biyo bayan jerin faretin sarauta da suka gudanar, yayin da jami’an tsaro suka buƙaci sanarwar kwanaki 72 kafin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jami’an tsaro na haɗin gwiwa a Kano sun yi barazanar kama Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da na 15, Aminu Ado Bayero.
Sun ce za su ɗauki mataki kan duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya ko tada hankalin jama’a a jihar Kano.

Source: Facebook
Kakakin rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a shafin na Facebook a jiya Juma'a.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta
Gargadin jami'an tsaro da Sanusi, Aminu Ado
Bayan wani taron gaggawa kan yanayin tsaro a jihar, jami’an sun ce za su gurfanar da duk mutum ko bangaren da ya karya dokar.
Dokar ta shafi hana hawan doki da gudanar da duk wani nau’in durbar a jihar Kano, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da umarni.
Da yake magana da ’yan jarida ranar Juma’a, Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce dokar tana nan daram.
Ya ce dokar hana hawan doki da duk wani nau’in durbar tana aiki kuma ta wajaba ga kowa a jihar, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
Bakori ya ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun lura da wasu abubuwan baya-bayan nan da ka iya kawo cikas ga doka da oda.

Source: Original
Abin da ya jawo lalata dukiyoyi a Kano
Gargadin jami’an tsaron ya zo ne bayan wani faretin sarauta da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gudanar a tsakiyar birnin Kano.
Rahotanni sun ce faretin ya kai ga lalata wasu kadarorin jama’a, ciki har da fastocin siyasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
’Yan sanda sun tabbatar da cewa lamarin ya haddasa tabarbarewar zaman lafiya, inda suka ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu.
Lamarin ya haifar da tashin hankali a tsakanin jama’a, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta hana hawan doki da duk wani nau’in faretin durbar a Kano.
Sai dai zaman lafiyar da ake samu ya sake fuskantar barazana ranar Alhamis, lokacin da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya hau farin doki.
Sanusi ya jagoranci daruruwan magoya bayansa a wani faretin sarauta zuwa bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai a filin wasa na Sani Abacha.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarci bikin, inda faretin Sanusi ya haifar da martani daga sansanin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Sansanin Bayero ya yi barazanar gudanar da cikakkiyar hawa bayan abin da ya bayyana a matsayin karya dokar hana hawan doki da ke aiki a jihar.
Barazanar ta fito ne daga wani babban mai ba da shawara ga Bayero, wanda kuma shi ne Sarkin Dawaki Babban na bangaren Bayero.
Wannan barazana ta sa jami’an tsaro suka sake fitar da umarni, inda suka ce ba za su bari wani abu ya kawo cikas ga zaman lafiya ba.
Da yake magana tare da Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, Abubakar Hussaini, Kwamishinan ’Yan Sandan ya bayyana sabon matsayar jami’an tsaro.
Gwamnatin Kano ta hana dukan nauyin hawa
An ji cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da dukkan jerin gwanon hawa da ayyukan hawan dawaki a cikin birnin Kano saboda dalilan tsaro.
Majalisar Tsaro ta Jihar ta ce yawan tattara magoya baya da ke da alaƙa da shirye-shiryen na iya haifar da arangama da karya doka.
Dakatarwar ta fara aiki nan take kuma za ta ci gaba da kasancewa har sai gwamnati ta ba da wata sanarwa.
Asali: Legit.ng

