Shugaba Tinubu Ya Yi Alhini da Aka Tabbatar da Rasuwar Tsohon Gwamma a Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar tsohon Gwamnan Gongola kuma tsohon shugaban PDP na kasa, Bamanga Tukur
- Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwar dattijon kasa a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja, yana da shekaru 90 a duniya
- Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Bamanga Tukur, Masarautar Fombina ta Adamawa, Gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijon ƙasa, fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Bamanga Tukur.
Tsohon gwamnan ya rasu ranar Asabar, 12 ga watan Satumba, 2026 a gidansa da ke Abuja yana da shekaru 90.

Source: Twitter
Vanguard ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Tukur, Tafidan Adamawa, a matsayin ƙarshen wani muhimmin babi a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan
Magana ta kare, INEC ta fitar da sunayen yan takarar shugaban ƙasa na ƙarshe kafin zaben 2027
Shugaban ya ce Tukur babban jigo ne wanda rayuwarsa ta shafi harkokin gudanar da mulkin jama’a, shugabanci, masana’antu, siyasa da jagoranci a harkokin kasuwanci a Afirka.
An haifi Bamanga Tukur ranar 15 ga watan Satumba, 1935. Ya yi fice a ƙasa baki ɗaya bayan zama Babban Manajan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya daga 1975 zuwa 1982.
Rahotanni sun nuna cewa ya taimaka wajen zamanantar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa da bunƙasa harkokin sufurin ruwa na Najeriya.
Tinubu ya tuna gudummuwar Bamanga Tukur
Shugaba Tinubu ya tuna da yadda Tukur ya shiga siyasa a lokacin Jamhuriya ta Biyu, lamarin da ya kai ga zaɓensa a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Gongola, wadda a yanzu ta ƙunshi jihohin Adamawa da Taraba, a 1983.
Bayan haka, marigayin ya yi fice a ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu inda ya rike matsayin Shugaban BHI Holdings da DADDO Group of Companies.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya ji ƙamshin nasara da ya samu gagarumin goyon baya gabanin zaben 2027
Ya kuma taɓa zama Ministan Masana’antu na Tarayya a ƙarƙashin gwamnatin Janar Sani Abacha daga 1993 zuwa 1995. A matakin nahiyar Afirka, Tukur ya kasance fitaccen mai fafutukar farfaɗo da tattalin arzikin Afirka.
Bamanga Tukur ya kasance Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa daga watan Maris 2012 zuwa Janairu 2014, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa
Shugaba Tinubu ya ce a lokacin da yake jagorantar PDP, Tukur ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya ta hanyar tabbatar da bin ƙa’idojin jam’iyya da gina matsaya ɗaya tsakanin ’ya’yanta.
Shugaba Tinubu ya ce:
“Alhaji Tukur mutum ne mai wayewa, karamci kuma mai zurfi wajen binnƙa’idojin gaskiya da hidima waɗanda Masarautar Adamawa da ƙasa baki daya ke alfahari da su.
"Mutum ne mai manyan manufofi da jarumtar kasuwanci wanda ya yi imani da irin damar da Najeriya ke da ita mara iyaka. Najeriya za ta yi matuƙar kewar shawarwarinsa na hikima da jagorancinsa na uba.”

Source: Twitter
Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Bamanga Tukur, Masarautar Fombina ta Adamawa, Gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa, da kuma daukacin al’ummar siyasa da ’yan kasuwa a Najeriya da faɗin Afirka.
Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa Tukur kura-kuransa, Ya ba shi Aljannar Firdausi, Ya kuma ba duk waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi.
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Zurmi
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, inda ya yaba da jajircewarsa wajen fuskantar matsalolin tsaro.
Tinubu ya bayyana marigayi sarkin a matsayin jagora mai kawo zaman lafiya, wanda shawararsa ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a Zamfara.
Asali: Legit.ng
