Abin da Aka Tattauna da Atiku, Obi domin Tsayar da Ɗan Takara 1 a 2027
- Kungiyar G100 na la’akari da yiwuwar zagaye na biyu a zaben 2027, yayin da kokarin sasanta Atiku Abubakar da Peter Obi kan dan takara guda ke ci gaba
- Atiku da Obi ba su nuna goyon baya ga tsarin dan takara guda ba, amma G100 na son ci gaba da tattaunawa domin hadin kan ‘yan adawa
- G100 ta ce idan babu wanda ya samu nasara a zagaye na farko, tattaunawar za ta taimaka wa jam’iyyun adawa su marawa dan takara guda baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Masu ruwa da tsaki na kawancen G100 na la’akari da yiwuwar gudanar da zagaye na biyu a zaben shugaban kasa na 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin shawo kan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi.

Kara karanta wannan
Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji

Source: Facebook
Majiyoyi daga Punch sun ce tattaunawar na ci gaba, yayin da G100 ke duba wasu hanyoyin hadin gwiwa idan ba a samu dan takara guda ba.
Shawarar da Kungiyar G100 ta bayar
Kungiyar ta gudanar da taronta na farko a ranar 31 ga Agusta a Abuja, inda jam’iyyun adawa suka halarta.
G100 ta fara da shawarar cewa jam’iyyun adawa su hada kai wajen tsayar da dan takara guda a zaben 2027.
Sai dai bangaren Atiku Abubakar da ke takara a ADC, da Obi, dan takarar NDC, sun ci gaba da rike burinsu na neman shugabancin Najeriya.
Wata majiya ta ce Atiku da Obi ba su nuna wata alamar amincewa da tsarin tsayar da dan takara guda ba a yanzu.
Sai dai G100 na son ci gaba da tattaunawa da su kafin zabe, lokacin zabe da bayan zabe domin samun hadin kai.
Majiyar ta ce shirin na iya kunsar yiwuwar gudanar da zagaye na biyu idan ba a samu wanda ya yi nasara kai tsaye ba.
Wata majiya ta daban ta ce yiwuwar zagaye na biyu na daga cikin tsare-tsaren kungiyar na tunkarar yanayi daban-daban.
Ta ce Atiku da Obi ba su mayar da hankali sosai kan shirin G100 na dan takara guda ba, amma har yanzu suna bukatar juna.
A cewar majiyar, binciken da G100 ta gudanar ya nuna cewa akwai yiwuwar kada a samu wanda ya lashe zaben kai tsaye.
Saboda haka, idan ba a samu dan takara guda ba, tattaunawar da ake yi za ta saukaka wa jam’iyyun adawa marawa dan takara daya baya.

Source: Facebook
Jam'iyyun adawa da suka halarci taron G100
A taron G100 na farko, wakilan ADC, APM, NDC, bangaren PDP karkashin Tanimu Turaki, PRP da SDP sun halarta, kamar yadda Vanguard ta ce.
Atiku, Obi da dan takarar APM, Seyi Makinde, ba su halarci taron ba, wanda aka shirya domin samar da tsarin hadin kan jam’iyyun adawa.
Sakataren yada labarai na bangaren PDP karkashin Tanimu Turaki, Ini Ememobong, ya tabbatar da cewa bangaren na ci gaba da goyon bayan shirin G100.
Ya ce PDP na ganin hada kan jam’iyyun adawa a matsayin hanyar tinkarar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mutanen Tinubu su dura kan Atiku
Mun ba ku labarin cewa kungiyar Tinubu Must Stay ta ce tana goyon bayan ci gaba da mulkin Shugaba Bola Tinubu, tana mai ambaton wasu bayanan tattalin arziki da shirye-shiryen gwamnati.
Kungiyar ta kawo karuwar GDP, shirin rancen karatu na NELFUND da sauya motoci zuwa CNG cikin abubuwan da ta ce ya kamata a duba yayin muhawarar siyasar 2027.
Hakan ya zo ne bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira da a kawo ƙarshen mulkin Tinubu a jawabinsa na ranar samun ’yancin kai.
Asali: Legit.ng

