"A Sauke Tuta," Gwamna Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki 3 bisa Rasuwar Alhaji Bamanga Tukur

"A Sauke Tuta," Gwamna Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki 3 bisa Rasuwar Alhaji Bamanga Tukur

  • Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana zaman makoki nankwanaki uku kan rasuwar Alhaji Bamanga Tukur
  • Fintiri ya umarci a sauke tutar jihar zuwa rabin sanda na tsawon kwanaki uku domin karrama marigayin
  • Tukur, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya rasu da sanyin safiyar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar kan rasuwar Bamanga Tukur, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola kuma tsohon shugaban PDP na ƙasa.

A matsayin girmamawa ga tsohon ɗan siyasar mai shekaru sama da 90, gwamnan ya kuma umarci a sauke tutar jihar zuwa rabin sanda na tsawon kwanaki uku.

Fintiri.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnati da ke Yola Hoto: @AUF
Source: Twitter

An fara makokin kwanaki 3 a Adamawa

Tukur, dattijo mai kishin ƙasa, ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan siyasa, ya rasu da sanyin safiyar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi alhini da aka tabbatar da rasuwar tsohon gwamma a Najeriya

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Humwashi Wonosikou, ya fitar ranar Asabar, Gwamna Fintiri ya bayyana rasuwar Tukur a matsayin babban rashi ga jihar Adamawa da Nijeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya ce marigayin ya bar gagarumar gudummawa da za ta dawwama wajen ci gaban siyasa da tattalin arziƙin ƙasar.

Fintiri ya yabi gudummawar Tukur

Fintiri ya yaba wa marigayin bisa jarumtaka, hangen nesa, kishin ƙasa da kuma sadaukarwar da ya yi tsawon rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Ya bayyana Tukur a matsayin ƙaton jigo a siyasar Nijeriya, wanda gudummawarsa ga jihar da ƙasar za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihin Nijeriya.

“Alhaji Bamanga Tukur babban jigo ne da ya bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban tsohuwar jihar Gongola, jihar Adamawa da Nijeriya.
“Gogewarsa, hikimarsa da sadaukarwarsa wajen yi wa al’umma hidima sun ba shi matsayi na musamman a tarihin ƙasarmu,” in ji Fintiri.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya ji ƙamshin nasara da ya samu gagarumin goyon baya gabanin zaben 2027

Gwamnan ya ce shi kansa zai yi kewar shawarwari da gogewar Tukur, musamman kan batutuwan da suka shafi jihar Adamawa da ƙasar baki ɗaya.

“Zan yi kewar shawarwarinsa masu hikima da zurfin gogewar da ya kawo wajen tattauna batutuwan da suka shafi jiharmu da ƙasarmu. Rasuwarsa ta bar babban gibi wanda zai yi wuya a cike,” in ji shi.
Bamanga Tukur.
Tsohon gwamna kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Bamanga Tukur Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Gwamna Fintiri ya mika sakon ta'aziyya

Fintiri ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Tukur, abokansa, abokan hulɗarsa da al’ummar jihar Adamawa, yana mai kira gare su da su samu ƙarfi daga kyakkyawan tarihin hidima da shugabanci da ya bari.

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa Tukur kura-kuransa, Ya ba shi Aljannar Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da masoyansa ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar tsohon Gwamnan Gongola kuma tsohon shugaban PDP na kasa, Bamanga Tukur.

Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Bamanga Tukur, Masarautar Fombina ta Adamawa, Gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa, da kuma daukacin al’ummar siyasa da ’yan kasuwa a Najeriya da faɗin Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262