Zaben 2027: Takarar Pantami Ta Gwamnan Gombe Ta Samu Babban Tagomashi

Zaben 2027: Takarar Pantami Ta Gwamnan Gombe Ta Samu Babban Tagomashi

  • Usman Kalala ya yi murabus daga shugabancin Labour Party a Gombe tare da komawa PDP, inda ya shiga jam’iyyar tare da Shehu Abubakar Durbi da magoya bayansu
  • Kalala da Durbi sun ce cancanta, gogewa da kwarewar jagorancin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne suka sa suka yanke shawarar komawa PDP
  • Sababbin ‘yan PDP din sun yi alkawarin tallafa wa Ibrahim Dankwambo da kuma yi wa dukkan ‘yan takarar PDP kamfen domin samun nasara a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Gombe ta samu karin karfi bayan Hon. Usman Sule Dauda, wanda aka fi sani da Kalala, ya yi murabus daga shugabancin Labour Party (LP) na jihar.

Kalala ya koma PDP tare da Hon. Shehu Abubakar Durbi da dimbin magoya bayansu, lamarin da jam’iyyar ta bayyana a matsayin babban ci gaba na siyasa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

Pantami ya samu tagomashi a Gombe
Farfesa Isa Ali Pantami da Sanata Ibrahim Dankwambo da masu sauya sheka zuwa PDP Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da da Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya sanya wa hannu kuma ya fitar a shafin Facebook na Farfesa Pantami ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026.

Kalala gogaggen dan siyasa ne da ya yi wa mazabar Kaltungo ta Yamma wakilci na wa’adi biyu a Majalisar Dokokin Jihar Gombe.

Ya kuma taba rike mukamin shugaban PDP na Karamar Hukumar Kaltungo kafin daga bisani ya zama shugaban LP na jihar Gombe.

Dalilin komawarsu PDP

A lokacin tarbar su a hukumance cikin PDP, Kalala da Durbi sun danganta matakin nasu da cancanta, kwarewa da gogewar jagoranci da suka ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami yake da su.

Sun bayyana kwarin gwiwarsu cewa Pantami, wanda ke neman zama gwamnan Gombe a karkashin PDP, zai samar da ingantaccen shugabanci tare da tabbatar da tafiyar da gwamnati cikin adalci da bai wa kowa dama.

Sun kuma yi imanin cewa jagorancinsa zai taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dawo da karfinsa, ya yi alƙawarin ƙuri'u miliyan 20 ga Tinubu

Durbi ya tabbatar da goyon baya

Hon. Shehu Abubakar Durbi na daga cikin fitattun ‘yan siyasar jihar, inda ya taba rike mukamin Kwamishinan Kula da Filaye da Safiyo na Jihar Gombe har sau biyu. Ya kuma taba wakiltar mazabar Gombe ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Gombe.

Durbi da Kalala sun bayyana cikakken goyon bayansu ga tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda aka fi sani da Talban Gombe.

Sun kuma yi alkawarin yin amfani da karfinsu wajen tattara magoya baya da gudanar da yakin neman zabe domin ganin dukkan ‘yan takarar PDP sun samu nasara a zaben 2027.

PDP ta yi maraba da sababbin ‘yan jam’iyyar

PDP ta ce komawar Kalala, Durbi da magoya bayansu na kara nuna yadda jam’iyyar ke samun karbuwa da kuma fadada karfinta a matakin kasa da kasa da kuma a tsakanin al’ummar jihar.

Jam’iyyar ta kuma ce matakin ya nuna karin hadin kai da karfin tafiyarta a matakin kasa, musamman yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara karfi.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim

A cikin sanarwar, PDP ta yi maraba da Hon. Shehu Durbi, Hon. Usman Kalala da magoya bayansu, tare da tabbatar musu da adalci da kyakkyawar mu’amala a cikin jam’iyyar.

Shugaban LP a Gombe ya koma PDP
Tsohon shugaban LP tare da su Farfesa Isa Ali Pantami Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Naja'atu ta musanta ba Pantami hakuri

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yar siyasa a Najeriya, Naja'atu Mohammed ta yi martani kan wani rahoton da ke cewa ta tura tawaga don ba dan takarar gwamnan Gombe na PDP hakuri.

Naja'atu ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta tura tawaga ta musamman domin ba Farfesa Isa Ali Pantami hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng