Shugaba Tinubu da APC Sun Shigar da Bukatar da Za Ta ba Atiku Matsala a Gaban Kotu
- APC da Shugaba Bola Tinubu sun roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Atiku Abubakar kan takardar shaidar NYSC
- Atiku da ADC sun nemi kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 saboda amfani da takardun bogi
- Lauyoyin Tinubu da APC sun ce babu wata shaida daga NYSC da ta nuna cewa takardar shaidar Tinubu ta bogi ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu sun roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da gaba ɗaya ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya shigar.
Atiku da ADC sun kai ƙarar Tinubu, APC da Hukumar Zaɓe, INEC, kan zargin cewa shugaban kasa ya gabatar wa INEC da takardar shaidar kammala hidimar ƙasa ta NYSC, ta bogi.

Kara karanta wannan
2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 ta nemi kotu ta hana Tinubu da APC, waɗanda su ne wanda ake ƙara na farko da na biyu, shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Atiku ya musanta amfani takardar bogi
A cikin takardar rantsuwa ta haɗin gwiwa da aka shigar ranar 9 ga Satumba, Tinubu da APC sun musanta cewa sun gabatar da wata takardar bogi ga INEC, ko dai a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ko na 2027.
Daraktan Sashen Shari’a na APC, Mista Sanusi Samaila, ya ce Shugaba Tinubu bai gabatar wa INEC da Form CF001 ba a zaɓen 2023 ko 2027 kamar yadda masu ƙarar suka yi iƙirari.
“Wanda ake ƙara na farko, Tinubu, ya musanta zargin masu ƙara na yin jabun takarda da kuma gabatar da takardar bogi ga INEC, a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ko 2027,” in ji shi.
Ya ce babu ɗaya daga cikin takardun da Tinubu ya gabatar wa INEC domin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da kuma mai zuwa na 2027 da aka yi na jabu.
'Atiku ba dan APC ba ne'
Ya ce Atiku ba dan jam'iyyar APC ba ne, kuma ba ɗan takara ba ne a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayu, wanda a cikinsa Tinubu ya zama ɗan takarar jam’iyyar.
Dangane da ikirarin Atiku da ADC kan cancantar Tinubu da kuma tsayar da shi a matsayin ɗan takarar APC, Samaila ya ce babu ɗaya daga cikin masu ƙarar da ya shiga zaɓen fidda gwani ko tsarin da APC ta bi wajen tsayar da ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Source: Facebook
“Masu ƙarar ba sa zargin a wanda ake ƙara na farko da na biyu sun karya wata tanadi na Dokar Zaɓe ko Kundin Tsarin Mulkin 1999, sai dai suna ƙorafin ne kan tsayar da wanda ake ƙara na farko (Tinubu) da gabatar da sunansa ga INEC."
“Haka kuma, masu ƙarar ba sa ƙalubalantar wata shawara, mataki ko aiki na INEC a cikin wannan ƙara,” in ji shi
Bisa haka ya bukaci kotun, a madadin Tinubu da APC, da ta yi watsi da wannan kara ta Atiku gaba daya domin ba ta cancanta ba.
Shugaban APC ya tafi hutun makonni 2
Kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya fara hutun makonni biyu a ƙasashen waje domin samun hutu da sake tsara dabarunsa.
A cewar jam’iyyar, hutun zai ba Yilwatda damar samun hutu, sake kuzari da kuma yin tunani kan manyan ayyukan da ke gabansa yayin da ake shirin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

