Hukumar NRS Mai Karbar Haraji na Daukar Ma'aikata? An Ji Bayanin Gaskiya
- Hukumar NRS ta ce sanarwar neman aikin da ake yaɗawa da sunan FIRS ta bogi ce kuma ba ta fito daga gare ta ba
- Sanarwar ta buƙaci masu neman aiki su tura CV da bayanan sirri zuwa wani adireshin imel, tare da wa’adin rufe aikace-aikacena ranar 24 ga Oktoba 2026
- NRS ta gargadi jama’a kada su biya kuɗi ko tura bayanan kuɗi, takardun shaida da sauran bayanan sirri ga masu sanarwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar tattara haraji ta kasa (NRS) ta gargadi ’yan Najeriya kan wata sanarwar bogi da ake yaɗawa a kafafen intanet, wadda ke ikirarin cewa tsohuwar FIRS na ɗaukar sababbin ma’aikata.
Sanarwar ta buƙaci masu sha’awar aikin su tura CV da takardun neman aiki zuwa wani adireshin imel, tare da bayar da bayanan sirri da takardun shaidar karatu.

Source: UGC
Sai dai a wata sanarwa da NRS ta fitar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 a shafinta na Facebook, hukumar ta ce saƙon na daukar ma'aikatan da za su cike gurbi ba shi da alaƙa da ita.
Hukumar NRS ta bayyana sanarwar daukar sababbin ma'aikatan a matsayin ta bogi.
“NRS na son bayyana karara cewa sanarwar ta bogi ce kuma ba ta fito daga hukumar tattara haraji ta kasa ba,” in ji hukumar.
NRS ta ce ba ta fara ɗaukar ma’aikata ba
Hukumar ta ƙara tabbatar da cewa ba ta ba da izinin fara aikin ɗaukar ma’aikata ba, kuma ba ta naɗa wani mutum, wakili, mai ba da shawara ko wasu ba domin gudanar da ɗaukar ma’aikata a madadinta.
“Domin kauce wa ruɗani, NRS ba ta ba da izini ko fara aikin ɗaukar ma’aikatan da aka ambata a sanarwar ba, kuma ba ta naɗa ko ba da izinin wani mutum, wakili, mai ba da shawara ko wasu ba ya gudanar da ɗaukar ma’aikata a madadinta ba,” in ji hukumar.
Hukumar ta tunatar da jama’a game da FIRS
Hukumar ta kuma tunatar da jama’a cewa NRS ta maye gurbin FIRS, don haka ta shawarci ’yan Najeriya da su yi watsi da duk wata sanarwar ɗaukar aiki da aka fitar da sunan FIRS.
Ta kuma bukaci masu neman aiki da su tabbatar da sahihancin bayanan ayyukan yi ta hanyar amfani da tashoshin sadarwa na hukuma.
An gargadi jama’a game da tura bayanan sirri
NRS ta gargadi jama’a kada su biya wani kuɗi, bayyana bayanan banki ko wasu bayanan kuɗi, ko kuma tura takardun shaida da takardun karatu saboda wannan sanarwar da ake zargin ta bogi ce.
Hukumar ta ce duk wani sahihin aikin ɗaukar ma’aikata da za ta gudanar za a sanar da shi a hukumance ta shafinta na yanar gizo da sauran hanyoyin sadarwa da aka amince da su.
NRS ta kuma ƙarfafa wa jama’a gwiwar kai rahoton duk wata sanarwar neman aiki da suke zargin ba ta da tushe ga hukumomin da suka dace.

Source: Facebook
Shugaban NRS ya magantu kan tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar NRS, Zacch Adedeji, ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mafi kyawun abu da ya faru da Najeriya.
Zach Adedeji ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ya dauka na cire tallafin tun a ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki a 2023.
Asali: Legit.ng


