An Samu Kuskure a Ƙarar Atiku kan Tinubu, Za a Sake Ɓallo Masa Ruwa

An Samu Kuskure a Ƙarar Atiku kan Tinubu, Za a Sake Ɓallo Masa Ruwa

  • Atiku Abubakar da ADC sun roƙi Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba su damar gyara ƙarar da suka shigar kan Tinubu da APC
  • Dan takarar shugaban kasa a ADC na neman a hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027 bisa zargin gabatar da takardar NYSC ta bogi ga INEC
  • Tinubu da APC sun musanta zargin, yayin da kotu ta sanya ranar 28 ga Satumba domin sauraron ƙarar da kuma buƙatar gyaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a ADC, Alhaji Atiku Abubakar ya roƙi Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba shi damar gyara ƙarar da ya shigar kan Bola Tinubu da APC.

Atiku da ADC sun roƙi Mai Shari’a Inyang Ekwo ya hana Shugaba Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 bisa zargin gabatar wa INEC takardar shaidar kammala hidimar NYSC ta bogi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da APC sun shigar da bukatar da za ta ba Atiku matsala a gaban kotu

Atiku ya tura roko ga kotu domin sabunta karar da ya shigar kan hana Tinubu takara
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Getty Images

Korafin Atiku, ADC kan takarar Tinubu

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, masu ƙarar sun maka Shugaba Tinubu, APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara na farko zuwa na uku, cewar Vanguard.

Tinubu da APC sun roƙi kotun ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya, suna cewa ba ta da inganci kuma masu ƙarar ba su da hurumin shigar da ita.

A cikin takardar rantsuwar amsa da suka gabatar ranar 9 ga Satumba, waɗanda ake ƙarar na farko da na biyu sun musanta gabatar da wata takardar bogi ga hukumar, ko a zaɓen 2023 ko 2027.

Su biyun, ta hannun Daraktan Shari’a na APC, Sanusi Samaila, sun ce ba su gabatar da Form CF001 ga INEC domin zaɓen 2023 ko 2027 kamar yadda masu ƙarar suka yi zargin ba.

Sun ce hukumar NYSC ba ta taɓa musanta bayar da takardar shaidar kammala hidimar NYSC ga Tinubu bayan ya kammala shekarar hidimarsa ba.

Kara karanta wannan

2027: Sanata Yari ya yanke hukunci kan wanda ya cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

Bukatar Atiku, ADC game da korafi kan Tinubu

A gefe guda, Atiku da ADC sun shigar da buƙatar a rubuce bisa tanadin sakin layi na 7(8) na Dokokin Kotun Tarayya kan shari’o’in gabanin zaɓe na 2006.

A cikin buƙatun biyu, sun roƙi kotun ta ba su izinin gyara takardar ƙarar da suka shigar tun farko.

Sun kuma roƙi kotun ta amince da sabuwar takardar ƙarar da aka gyara a matsayin ingantacciyar takardar ƙarar da aka yi wa gyara.

Masu ƙarar sun bayyana dalilai huɗu da ya sa ya kamata a amince da buƙatarsu, inda suka ce sun shigar da ƙarar ranar 14 ga Agusta.

Atiku da ADC sun ce bayan shigar da ƙarar, sun gano wasu kura-kurai, musamman sunan fom ɗin INEC da aka haɗa da rantsuwar, wanda aka kira Form CF001 maimakon sabon Form EC9A.

Sun ce akwai kuma buƙatar fayyace bayanan zargin damfarar da suka gabatar a cikin rantsuwar, tare da rubutacciyar shaida daga Atiku da kuma ƙarin kwafe-kwafen wasu takardu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya bukaci Tinubu ya janye daga takarar 2027

Sun ce za a maye gurbin wasu daga cikin takardun da aka haɗa a baya da sababbi, domin waɗanda suka gabatar da ƙarar ba su samu cikakkun kwafe-kwafen ba lokacin shigar da ƙarar.

Tinubu, APC za su kwaba wa Atiku aiki

Mun ba ku labarin cewa APC da Shugaba Bola Tinubu sun roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Atiku Abubakar kan takardar shaidar NYSC Atiku da.

ADC sun nemi kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 saboda amfani da takardun bogi.

Lauyoyin Tinubu da APC sun ce babu wata shaida daga NYSC da ta nuna cewa takardar shaidar Tinubu ta bogi ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.