Kotu Ta Dauki Mataki kan Bukatar Atiku Ta Hana Tinubu Takara a 2027

Kotu Ta Dauki Mataki kan Bukatar Atiku Ta Hana Tinubu Takara a 2027

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 28 ga Satumba domin ci gaba da sauraron ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar domin hana Bola Tinubu takara
  • Ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, ta ƙunshi zargin cewa Tinubu ya gabatar da takardar shaidar kammala yi wa ƙasa hidima ta NYSC da ake zargin bogi ce
  • Atiku, tare da ADC a matsayin mai ƙara ta biyu, sun nemi kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027, yayin da INEC ce mai ƙara ta uku a shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya shigar kan cancantar Shugaba Bola Tinubu ta sake neman wa’adin mulki a 2027.

Kara karanta wannan

IPOB ta yi barazanar da za ta shafi zaben 2027 kan Nnamdi Kanu

Mai shari’a Inyang Ekwo ya sanya ranar 28 ga Satumban 2026 domin ci gaba da shari’ar, bayan lauyoyin ɓangarorin sun gabatar da matsayinsu kan yadda za a gudanar da shari’ar.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Zargin da Atiku ya yi wa Tinubu

Vanguard ta rahoto cewa a cikin shafi 25 na bayanain da Atiku da kansa ya gabatar domin goyon bayan ƙarar, ya zargi Tinubu da gabatar wa INEC takardar shaidar NYSC da ya ce ta bogi ce.

Atiku ya ce takardar da aka gabatar wa INEC tana ɗauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle”, yayin da ya ce sunan Shugaba Tinubu ba Adekunle ba ne.

Channels TV ta wallafa cewa ya ce takardar tana hannun INEC kuma an yi amfani da ita wajen nuna cewa Tinubu ya cika sharudan tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Atiku ya kuma yi zargin cewa Tinubu ya kasance yana amfani da wannan takarda tun shekarar 1999, lokacin da ya tsaya takarar gwamnan Jihar Legas.

Batun hana Tinubu takara

Masu ƙarar sun bukaci kotu ta yanke hukunci kan ko gabatar da takardar da suke zargin ta kasance ta bogi ya sa Tinubu da APC ba su cancanci shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da 2027 ba.

Kara karanta wannan

2027: An samu matsala a taron hadakar jam'iyyun adawa domin kifar da Tinubu

Sun kuma nemi kotu ta ayyana cewa Tinubu ya karya tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ya shafi cancantar ɗan takarar shugaban ƙasa idan ya gabatar da takardar shaidar bogi.

Bugu da ƙari, sun nemi kotu ta bayar da umarnin hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027 saboda zargin gabatar da takardar NYSC da ba ta dace da sunansa ba.

Atiku Abubakar da abokin takarar shi.
Lokacin da Atiku Abubakar ya gana da Rotimi Amaechi. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Nafiu Bala ya soki Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɓangaren ADC da Hon. Nafiu Bala ke jagoranta ya ƙi duk wani yunƙuri na danganta Atiku Abubakar da suna, tambari da sauran alamomin jam’iyyar.

Tsagin jam’iyyar ya kuma bayyana cewa ba zai shiga wani ƙawance, haɗaka ko haɗin gwiwa da wata jam’iyyar siyasa gabanin babban zaɓen 2027 ba.

Bayan wani taron gaggawa na BOT da NWC da aka gudanar ranar Litinin, jam’iyyar ta zargi Atiku da amfani da sunanta da alamominta ba tare da izini ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng