"Baka Cancanci Mulkin Najeriya ba", Fasto Daga Legas Ya Soki Mulkin Tinubu

"Baka Cancanci Mulkin Najeriya ba", Fasto Daga Legas Ya Soki Mulkin Tinubu

  • Fasto Primate Elijah Ayodele ya ce Najeriya ba ta samu cikakken ’yancin kai ba saboda rashin ingantaccen shugabanci
  • Ya soki gwamnatin Bola Tinubu tare da cewa tikitin Muslim-Muslim ba ya nuna ’yanci, sai dai “kangin rayuwa” da ake ciki
  • Ayodele ya ce sake fasalin Najeriya ne kaɗai zai iya kawo cikakken ’yancin kai, amma ya zargi gwamnati da guje wa batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Oka Afa, Jihar Legas — Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce har yanzu Najeriya ba ta samu cikakken ’yancin kai ba, yana mai alakanta matsalolin ƙasar da rashin ingantaccen shugabanci.

Faston ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta na nuna cewa ƙasar ba ta kai ga samun cikakken ’yancin kai ba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar tare da aikawa Legit.ng ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, Ayodele ya ce abin da ’yan Najeriya ke da shi ba cikakken ’yancin kai ba ne.

Kara karanta wannan

Malamar addini ta fito ta gayawa Tinubu gaskiya kan halin da ake ciki a Najeriya

Faston Legas ya yiwa Tinubu wankin babban bargo
Ayodele ya soki mulkin Tinubu | Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya bayyana shi a matsayin “’yancin kai na rashin ci gaba da yunwa”.

Ayodele ya soki Tinubu

Ayodele ya ce gwamnatin Najeriya ta fi mayar da hankali wajen yin korafi kan matsalolin ƙasar maimakon samar da mafita.

Ya kuma ce Shugaba Tinubu ba shi da cancantar jagorantar ƙasar, yana mai cewa hakan ya hana ’yan Najeriya jin daɗin ’yancin kai.

A cewar Ayodele:

“Tinubu bai cancanci zama shugaban ƙasa ba, saboda haka babu yadda mutane za su ji daɗin ’yancin kai.
“Gwamnatinmu tana yawan yin korafi alhali ya kamata ta samar da mafita. Wannan ’yancin kai lokaci ne na sake tunani, amma shugaban ƙasa bai shirya yin hakan ba.”

Ya yi magana kan sake fasalin kasa

Faston ya kuma soki tsarin tikitin Muslim-Muslim da Shugaba Tinubu ya yi amfani da shi wajen neman shugabancin Najeriya.

Ayodele ya ce tsarin ba ya nuna ’yanci, sai dai ya kira shi wani nau’in kangin rayuwa.

Kara karanta wannan

Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai

Ya ce sake fasalin Najeriya ne kaɗai zai iya kawo cikakken ’yancin kai, amma gwamnati ba ta shirya fara wannan tattaunawar ba.

Ya kara da cewa:

“Babu ’yanci a duk abin da muke yi. Tikitin Muslim-Muslim ba ’yancin kai ba ne, kangi ne.
“Hanya ɗaya tilo da za mu samu ’yancin kai ita ce ta hanyar sake fasalin Najeriya, amma gwamnati ba ta shirya hakan ba. Idan aka duba ababen more rayuwa, lafiya, tattalin arziki da sauran abubuwa, kangi ne kawai.”

Ya soki gwamnati kan matasa

Ayodele ya kuma zargi gwamnatin tarayya da rashin kyakkyawan tsari da kuma gazawa wajen samar da makoma ga matasan Najeriya.

Ya bayyana gwamnatin a matsayin mai son kai da rashin tsari, yana mai cewa hakan na daga cikin dalilan da ya sa ƙasar ba ta kai ga cikakken ’yancin kai ba.

Ya ce:

“Gwamnatin tana da son kai kuma ba ta kula. Ba gwamnati ce mai tsari ko shiri ba, shi ya sa har yanzu muke cikin tsarin neman ’yancin kai."

Ya ƙara da cewa babu yawan addu’o’in da za su magance matsalar ƙasar idan shugabanci bai inganta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng