Babbar Magana: An Yi Yunkurin Kashe Dan Takarar Gwamna na Jam'iyyar PDP a Najeriya
- PDP reshen jihar Cross River ta zargi wasu ‘yan daba da kai hari kan ayarin dan takararta na gwamna, Sir Arthur Javis-Archibong, a Kalaba ta Kudu
- Javis-Archibong ya ce an kai wa ayarinsa hari a wurare biyu, inda mutane uku suka jikkata tare da lalata motoci
- Jam’iyyar ta ce magoya bayanta sun kaurace wa ramuwar gayya, yayin da ‘yan sanda ke tabbatar da rahotannin harbe-harbe da jikkatawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Calabar, Cross River - Jam’iyyar PDP a Jihar Cross River ta zargi wasu ‘yan daba da yunkurin hallaka dan takararta na gwamna a zaben 2027 da ke tafe, Sir Arthur Javis-Archibong.
PDP ta yi wannan zargin ne bayan wasu yan daba sun kai hari kan ayarin dan takarar takararta na gwamna, Sir Arthur Javis-Archibong, yayin rangadin tuntubar jama’a da jam’iyyar ta gudanar a karamar hukumar Kalaba ta Kudu ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗauki zafi, 'yan daba dauke da bindigu sun buɗe wa magoya bayan PDP wuta

Source: Facebook
Da yake magana kan abin da ya faruJavis-Archibong ya ce ‘yan maharan sun kai wa ayarinsa hari a wurare biyu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya bayyana cewa hari na farko shi ne a fadar Sarkin Calabar ta Kudu, Etubom Nyong Edet Okon 1, inda mutane uku suka jikkata.
Ya ce daga bisani an sake kai wa ayarin hari a awurin yaro a African Club da ke kan titin Kalaba, inda aka lalata motoci tare da harbe-harbe kan ayarin.
PDP ta bayyana abin da ya faru
A cewar Javis-Archibong, kimanin magoya baya 3,000 ne suka halarci taron PDP, wanda aka sanar da ‘yan sanda a hukumance, amma duk da haka wasu bata-gari sun tarwatsa tarurrukan tare da bude wuta kan mambobin jam’iyyar.
“Mun hana magoya bayanmu daukar fansa saboda mun yi imani da bin doka da oda. Maimakon mu mayar da martani, mun nufi ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda kai tsaye da ayarinmu domin neman kariya,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: 'Yan ta'adda sun rutsa manoma 15, sun masu mummunan aiki babu daɗin gani
Sakataren Yada Labarai na PDP a jihar, Prince Mike Ojisi, ya bayyana lamarin a matsayin “hari mai tayar da hankali” kan harkokin dimokuradiyya
Ya bukaci hukumomin tsaro su gano, kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata lamarin.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar PDP da su “zauna lafiya tare da kauce wa duk wani mataki na ramuwar gayya.”
APC ta musanta hannu a harin
A nata bangaren, Jam’iyyar APC ta musanta hannu a lamarin ta bakin Sakataren Yada Labaranta na jihar Cross River, Emmanuel Inyang, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Facebook
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Cross River ta ce an tura jami’anta zuwa wuraren da lamarin ya faru, inda ta tabbatar da cewa halin da ake ciki komai yana karkashin iko.
Rundunar ta kuma ce tana gudanar da bincike kan rahotannin harbe-harbe da jikkata mutane da aka yi domin tabbatar da sahihancinsu.
An kai hari wurin taron ADC
Kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wurin da ake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC a jihar Cross River.
An ruwaito cewa tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da wani jami'in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) yayin harin da suka kai.
Asali: Legit.ng