Jam'iyyar APC Ta Shiga Rudani kan Kalubalantar Nasarar Gwamna Adeleke a Osun
- Tawagar lauyoyin APC a Osun ta musanta cewa ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen gwamnan jihar
- Lauyan APC, Adekunle Adegoke SAN, ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar barin sakamakon zaɓen, duk da cewa akwai wasu dalilan da za a iya ƙalubalantar sa
- Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen Osun ta nuna cewa akwai ƙorafe-ƙorafe biyu da aka shigar, ciki har da wanda aka rubuta da sunan APC da ɗan takararta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Tawagar lauyoyin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Osun ta musanta cewa ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen gwamnan jihar.
Hakan na zuwa ne bayan an bayyana cewa akwai ƙorafe-ƙorafe biyu da aka shigar gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamnan Osun.

Source: Twitter
A cewar sanarwar da Sakataren kotun, Belemo Diete-Spiff, ya sanya wa hannu, ƙorafi na farko na ɗauke da lambar EPT/Os/Gov/01/2026, cewar rahoton The Punch.
Sunayen APC da Oyebamiji sun bayyana
A cikin ƙorafin farko, an bayyana ɗan takarar APC na gwamnan Osun, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da APC a matsayin masu ƙara.
An kuma bayyana Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, Accord Party da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara.
Sanarwar ƙorafe-ƙorafen biyu an manna ta ne a allon sanarwa na kotun da ke harabar Babbar Kotun Jihar Osun a Osogbo ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026.
Lauyan APC ya ce ba su shigar da ƙara ba
Sai dai Adekunle Adegoke SAN, ɗaya daga cikin jagororin tawagar lauyoyin APC, ya ce babu wata ƙara da aka shigar a madadin Oyebamiji ko jam’iyyar APC.
Adegoke ya bayyana cewa tawagar lauyoyin ta yanke shawarar ba za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen ba, duk da cewa sun gano wasu abubuwan da za a iya amfani da su wajen ƙalubalantar sakamakon.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gano abin da ya hana a magance rashin tsaro a Najeriya
Ya ce tawagar ta ƙunshi manyan lauyoyi, ciki har da Dr Biodun Layoonu SAN, Dr Yomi Aliyu SAN, Dr Muritala Abdulrasheed SAN da shi kansa.
Lauyan ya ƙara da cewa akwai wasu ƙwararrun malaman shari’a a cikin tawagar, ciki har da Farfesa Mojeed Alabi, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.
“Mun zaɓi zaman lafiya”
Adegoke ya ce tun bayan sanar da sakamakon zaɓen ranar 16 ga Agusta, tawagar ta shawarci abokin aikinta cewa abin da ya fi dacewa shi ne kada a kai ƙarar zuwa kotun zaɓe.
Ya ce ba wai sun yanke shawarar hakan saboda zaɓen ya kasance ba tare da kura-kurai ba ne, domin akwai wasu dalilai da za a iya amfani da su wajen ƙalubalantar sakamakon.
Sai dai ya ce APC ba ta son a ɗauke ta a matsayin jam’iyyar da ke kai ƙara kawai domin haifar da rikici ko hayaniya a tsakanin jama’a.
Ya ce Oyebamiji ya taya Adeleke murna
Adegoke ya bayyana cewa Oyebamiji ya taya Adeleke murnar nasarar da ya samu, kuma hakan ya nuna matsayar ɗan takarar APC na barin lamarin ya wuce.
Ya tambayi yadda za a ce Oyebamiji ya taya Adeleke murna da kansa, sannan daga baya ya ba da umarnin shigar da ƙara a ɓoye.
Ya ce takardar da wasu mutane suka gabatar a matsayin ƙarar APC ba ta samu izini daga jam’iyyar ko ɗan takararta ba.

Source: Facebook
Adegoke ya bayyana waɗanda suka shigar da takardar a matsayin mutanen da ke kwaikwayon lauyoyin APC, yana mai cewa tawagar shari’ar jam’iyyar ta yi watsi da dukkan takardun da aka gabatar ba tare da izininta ba.
Ya ce matakin APC na barin sakamakon zaɓen ya tsaya ya samo asali ne daga burin bai wa al’ummar Osun damar samun zaman lafiya da kuma shirya kanta cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Oyebamiji ya amince da shan kaye
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan APC a zaben Osun, Bola Oyebamiji ya amince da sakamakon zaben.
Bola Oyebamiji ya bayyana cewa duk da kammala zaben, har yanzu ya kuduri aniyar ci gaba da yi wa Osun hidima.
Asali: Legit.ng

