Peter Obi na Neman Mulkin Najeriya, Gwamnatin Anambra Ta Kunno Masa Wuta a Gida

Peter Obi na Neman Mulkin Najeriya, Gwamnatin Anambra Ta Kunno Masa Wuta a Gida

  • Gwamnatin Anambra ta zargi Peter Obi da ƙoƙarin rusa APGA tun bayan barinsa jam’iyyar a 2014, tana kira ga magoya bayanta su kare jam’iyyar
  • Ta ce kada magoya bayan APGA su zaɓi Obi da NDC, yayin da ake ci gaba da samun takaddama tsakaninta da tsohon gwamnan.
  • Rikicin ya kuma shafi batun basussukan da ake zargin gwamnatin Obi ta bari, wanda tsohon gwamnan ya musanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta buƙaci magoya bayan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) da su kare tushen siyasarsu tare da bijire wa NDC da Peter Obi gabanin babban zaɓen 2027.

Gwamnatin ta zargi Peter Obi da kokarin rusa jam'iyyar APGA wadda ya rike mukamin gwamnan Anambra a cikinta.

Peter Obi ya samu matsala da gwamnatin Anambra
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 mai taken “A Betrayal Alert for Ndi APGA”,

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake

Ta yi zargin cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, ya kasance yana ƙoƙarin rusa APGA tun shekarar 2014.

Gwamnati ta soki Peter Obi

A cikin saƙon, gwamnatin ta ce zaɓen Peter Obi da NDC tamkar zaɓen rusa jam'iyyar APGA ne.

“Zaɓen Peter Obi da NDC zaɓi ne na kashe APGA,” in ji saƙon.

Gwamnatin ta kuma yi zargin cewa tun 2014, Obi yana da burin rusa jam’iyyar da ta ba shi damar zama gwamnan Anambra.

Ta ƙara da cewa a 2025, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya tsaya tare da APGA, Obi ya goyi bayan masu adawa da jam’iyyar.

“Kar ku bari mutumin da ya bar gidansa ya ruɗe ku. Anambra ta APGA ce. ’Yan APGA, ku kare gidanku. Ku bijire wa NDC,” gwamnatin ta ce.

Tarihin Peter Obi da APGA

Peter Obi ya kasance gwamnan Anambra daga watan Maris na 2006 zuwa Maris na 2014, duk da cewa wa’adinsa na farko ya samu tangarda bayan an tsige shi daga mukami a watan Nuwamban 2006.

Kara karanta wannan

An fara murna da gwamnatin Tinubu ta cika alkawarin da ta daukarwa sojojin Najeriya

A watan Oktoban 2014, Obi ya fice a hukumance daga APGA, sannan ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A watan Mayun 2022, ya fice daga PDP domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party.

A zaɓen 2023, Obi ya zo na uku, bayan Atiku Abubakar na PDP da Bola Tinubu na APC, wanda daga bisani aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Obi ya koma ADC sannan NDC

A watan Disamban 2025, tsohon gwamnan Anambra ya fice daga Labour Party ya koma African Democratic Congress (ADC).

Kusan watanni biyar bayan haka, Obi da Rabiu Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na New Nigeria Peoples Party (NNPP), suka sanar da komawarsu New Democratic Congress (NDC).

Tun bayan hakan, Obi da gwamnatin Anambra sun shiga takaddama kan batun basussukan da ake zargin gwamnatinsa ta bari.

Gwamnatin Anambra ta ragargaji Peter Obi
Peter Obi na jawabi a ranar 'yancin kai Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Peter Obi ba zai sayi kuri'u ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Peter Obi ya ce takararsa ba za ta shiga harkar sayen ƙuri’u gabanin babban zaɓen 2027 ba da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng