Abin Mamaki: Za a Nema wa Tinubu, Shettima Kuri’u Miliyan 50 a 2027
- Jam’iyyar APC ta ce tana shirin tattara miliyoyin kuri’u domin tallafa wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimaki Kashim Shettima a zaɓen 2027
- Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, za ta jagoranci taron mata sama da 20,000 a Abuja domin tsarin yaƙin neman zaɓe
- APC ta ce shirye-shiryen NELFUND, CREDICORP, ayyukan tituna da tallafin tsabar kuɗi na daga cikin abubuwan da za ta gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC ta ce kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 na shirin tattara ‘yan Najeriya miliyan 50 domin sake zaɓen Tinubu da Shettima.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ake sa ran za ta jagoranci taron shugabannin mata da ƙungiyoyin ƙasa a Abuja.

Source: Facebook
Taron zai gudana ne a Cibiyar Taron Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu, inda ake sa ran sama da mata 20,000 daga faɗin Najeriya za su halarta, cewar TVC News.
Yadda aka shirya gangami saboda Tinubu, Shettima
Taron zai haɗa shugabannin mata, ƙwararru, ’yan kasuwa da masu shirya ayyukan al’umma domin tattauna manufofin gwamnati da ƙarfafa mata kafin zaɓen 2027.
Gimbiya Gloria Akobundu, mamba a kwamitin tsare-tsaren wayar da kan mata na APC, ta ce za a bayyana shirye-shiryen gwamnati da ta ce sun amfani miliyoyin ’yan Najeriya.
Ta ambaci Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND), ayyukan more rayuwa, shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu, lamunin masu saye da fasahar zamani.
Akobundu ta ce NELFUND ya yi rajistar ɗalibai sama da miliyan 1.4, yayin da aka samu buƙatun lamuni sama da miliyan 1.69 daga masu neman tallafi.
Ta ce sama da naira biliyan 191 aka raba ta hanyar cibiyoyin ilimi sama da 320, domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗin karatu.

Source: Facebook
Shirye-shiryen da za a tallata Tinubu da su
Ta kuma bayyana shirin CREDICORP a matsayin wani shiri da ke ba ’yan Najeriya damar samun lamuni domin bukatun kansu, ilimi, gyaran gidaje da makamashi mai sabuntawa.
Dangane da ayyukan more rayuwa, Akobundu ta ce gwamnatin tarayya ta gina sama da kilomita 2,700 na manyan tituna, yayin da wasu manyan ayyukan hanya da layin dogo ke ci gaba.
Ta ce Shirin Tallafin Kuɗi Kai Tsaye na Sabunta Fata, wanda aka ƙaddamar bayan cire tallafin man fetur, yana taimaka wa iyalan da ke cikin mawuyacin hali.
Akobundu ta ce mata na bukatar fahimtar ayyukan gwamnatin tare da isar da saƙon Sabunta Fata zuwa kowace al’umma, gunduma da rumfar zaɓe, cewar Daily Post.
APC a Taraba za ta yiwa Tinubu gata
An ji cewa APC a Taraba ta sha alwashin tattara kuri’u domin Bola Tinubu da sauran ‘yan takararta a zaben 2027, duk da tashe-tashen hankulan siyasa.
Shugaban APC na jihar, Abubakar Bawa, ya ce jam’iyyar za ta kai yakin neman zabe gidaje, masallatai, coci-coci da kananan hukumomi.
Tompolo da Gwamna Agbu Kefas sun nemi al’ummar Taraba su sake bai wa Tinubu dama, suna cewa ci gaba da mulki zai karfafa ayyukan ci gaba.
Asali: Legit.ng

